FIFA ta yi watsi da ƙorafin Nijeriya kan aike wa imel ɗin da ba ta amince da shi ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa FIFA, ta yi watsi da ƙorafin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) akan rikicin wasanta da DR Kongo na neman gurbi, saboda NFF ɗin ta yi kuskuren tura wa wani adireshin Imel da ba shi ta amince wa ba.

A madadin amfani da shafin shari’ar FIFA na yanar gizo, NFF ta tura ƙorafin nata ne ta wani adireshin Imel da ake amfani da shi a ofishin Babban Sakataren hukumar ƙwallon ƙasa-da-ƙasar. Wannan kure da ya haifar da jinkirin isarwa da kuma watsi da ƙorafin daga bisani akan rashin cika ƙa’ida da jinkirin shigarwa.

Nijeriya ta sha kaye ne a wasan neman gurbi shiga gasar Kofin Duniya na 2026 a birnin Rabat na ƙasar Moroko, wanda DR Kongo ta yi nasarar da ci 4 da 3 a bugun fenareti bayan tashi wasan 1 da 1 tsakanin ɓangarorin biyu.

NFF ta yi ƙorafin ne bisa ƙalubalantar sahihancin shigar mai tsaron gidan Kongo, Lionel Mpasi cikin tawagar ‘yan wasan, wanda aka yi zargin bai cika sharuɗɗan zama cikakken ɗan ƙasar ba daga Faransa gabanin shiga wasan.

Wasu binciken da rahotanni suka bayyana sun nuna cewa jami’an shari’ar FIFA sun samu Mpasi da rashin cika ƙa’idar sauya ƙasa. An dai yi watsi da ƙorafin Nijeriyar ne akan saɓa wa hanyar aike da kuma yin hakan a ƙurarren lokaci.

By Babaji

Leave a Reply