Daukar dubban matasa aiki a 123 Homes na rage wa gwamnati nauyi — Tajuddeen UAC

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

An bayyana cewa duk wata masana’anta ko kamfani da makamantansu da suka ɗauki matasa aiki, to hakan na rage wa gwamnati nauyi ne.

Saboda haka, shugaban kamfanin gine-gine da samar da filaye domin amfanin al’umma, kuma Manajan Darakta na 123 Homes & Facility Managers Ltd, Alhaji Tajudden Musa UAC, ya ce kamfaninsu ya ɗauki ɗimbin matasa aiki domin bunƙasa tattalin arzikin al’umma da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce kamfanin na ƙoƙarin tabbatar da cewa ana gudanar da komai bisa tanadin doka, ta hanyar biyan dukkan haƙƙoƙin gwamnati da sauran hukumomi a kowane mataki.

Ya ce suna ganin wannan dama ce da gwamnati za ta yi amfani da ita wajen taimaka wa al’ummar ƙasa, tare da taimaka wa irin waɗannan kamfanoni da masana’antun da suke samar da ayyukan yi ga jama’a domin samar musu da kyakkyawar makoma.

Ya ce burin kowace gwamnati shi ne ’yan ƙasa su samu abin yi, saboda haka ya kamata a tallafa wa kamfanoni masu samar da ayyukan yi.

Haka kuma, ya ce 123 Homes na karɓar ɗalibai daga manyan makarantu, musamman waɗanda suka karanci fannoni da suka shafi gine-gine da makamantansu, domin su zo su ci gaba da karatunsu a aikace.

Ya ce a ƙoƙarinsu na ganin al’umma ta samu aikin yi, suna tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da cewa waɗanda suka samu damar shiga kamfanin sun koyi sana’a da yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa domin ƙarfafa gwiwar ma’aikatan, suna biyan su albashin da ya dace da su, sannan suna bin diddigin halin da suke ciki, inda idan suka lura ba su ga wani mutum ba, sukan bi diddigin halin da yake ciki, ko yana fama da rashin lafiya ko kuma wata matsala.

Ya ce hakan na daga cikin abubuwan da ke nuna mutuntaka, hankali, tausayi da sanin ya kamata.

A ƙarshe, Musa UAC ya ce babban burinsu shi ne buɗe sassa daban-daban da suka shafi gine-gine da kuma samar da kayan amfanin gida, ta yadda ɗaruruwa ko dubban matasa za su samu aikin yi.

Ya ce hakan na da muhimmanci musamman idan aka yi la’akari da ɗimbin matasan da ba su da aikin yi a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce suna da kyakkyawar alaƙar aiki da Ma’aikatar Filaye da Safiyo, da Ma’aikatar Kula da ƙananan Hukumomi da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin tabbatar da cewa ana gudanar da ayyuka bisa doka.

Ya kuma yi wa Nijeriya fatan alheri, tare da fatan ganin ƙasa ɗaya da al’umma ɗaya yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai.

By ukarofi