Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ma’aikatan da ke ƙarƙashin ƙungiyar Support Staff Union ta Kamfanin Matatar Mai na Fatakwal (PHRC), sun yi barazanar rufe ayyukan matatar idan ba a biya su albashin watanni bakwai da ake binsu ba, tare da aiwatar da sabon tsarin albashin da suka ce an amince da shi.
Ma’aikatan sun gudanar da zanga-zanga tare da tare ƙofar shiga matatar, inda suka ce idan ba a biya bukatunsu cikin sa’o’i 48 ba, za su rufe matatar gaba ɗaya.
Sun kuma buƙaci a aiwatar da sabon tsarin albashi da alawus-alawus da suka ce GCEO na NNPC, Bayo Ojulari, ya amince da shi daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, tare da biyan bashin albashin watanni bakwai da kuma amincewa da tallafin gidaje ko haya na naira miliyan ɗaya.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan, Bennett Isy, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sa baki a lamarin, yana mai cewa ƙungiyar ba za ta ja da baya ba.
Ya ce idan ba a aiwatar da bukatunsu cikin sa’o’i 48 ba, za su hana kowa shiga harabar matatar.
Wata ma’aikaciyar, Joy Osueiya, ta ce ma’aikatan sun ƙi amincewa da shawarar dage aiwatar da sabon tsarin albashin zuwa Janairu 2027, tana mai cewa lokaci ya yi nisa.
Ta kuma yi zargin cewa wasu ma’aikata sun fuskanci matsalolin lafiya da jikkata sakamakon haɗarin da ke tattare da aiki a matatar.
Wani ma’aikaci, Godspower Nwakanji, ya roƙi Shugaba Tinubu da ya sa baki domin kawo ƙarshen matsalar.
A cewar NNPC, a halin yanzu an dakatar da aikin Matatar Mai ta Fatakwal domin gudanar da ayyukan gyare-gyare.
