Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Sakamakon kyakkyawan tsarin karatun da Afrika Academy da ke Kano ke gudanarwa ta hanyar sadarwa ta zamani, wato intanet, ko kuma tsarin karatun online, wata tsohuwa mai shekaru 67 da ke Jihar Kaduna ta samu takardar shaidar kammala karatun ƙwarewa na Diploma a kan ilimin addinin Musulunci.
Malam Rabiu Yusuf, Shugaban Afrika Academy, ya bayyana cewa tsohuwar ta kammala karatun ne a fannoni shida da suka haɗa da Tafsiri, Sirar Ma’aiki (SAW), Tauhidi, Hadisi, Fiƙihu da kuma ilimin Tarbiyya domin kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma.
Ya kuma bayyana cewa wani soja da ke fagen fama a Maiduguri, inda yake fafatawa da ’yan Boko Haram, shi ma ya kammala irin wannan Professional Diploma a kan ilimin addinin Musulunci.
Shugaban Afrika Academy ya bayyana hakan ne bayan bikin yaye ɗalibai 3,500 da makarantar ta gudanar a shekarar 2026, wanda ya kasance karo na biyu a tarihin wannan tsangaya da ke Kano.
Haka kuma, Malam Rabiu ya ce a shekarar 2025 da ta gabata, tsangayar ta yaye ɗalibai 2,200.
Ya bayyana cewa daga cikin ɗalibai goma da suka nuna ƙwazo a shekarar 2025, an bai wa waɗanda suka yi fice kyaututtuka, inda ɗalibi na farko ya samu kyautar kujerar Umrah, na biyu ya samu dala 500, na uku dala 300, na huɗu dala 200, sannan na biyar ya samu dala 100.
Ya ce a shekarar 2026 ma, ɗalibai 13 sun samu kyaututtuka sakamakon ƙwazonsu a makarantar, inda ɗalibai na farko zuwa na biyar suka samu kyautar kujerar Umrah, yayin da ɗalibai daga na shida zuwa na 13 suka samu kyautar dala 100 kowannensu.
Ya ƙara da cewa wasu ɗalibai huɗu kuma sun samu kyaututtukan kayan aure da kuma biyan kuɗin haya na tsawon shekara guda kowanne nsu.
Ya ce ana bayar da irin waɗannan kyaututtuka ne domin jawo hankalin matasa da sauran al’umma su yi wannan muhimmin karatu da zai amfani rayuwarsu.
Malam Rabiu ya bayyana cewa ana kammala wannan karatu cikin shekara guda ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani, wato online studies.
Ya ce Afrika Academy tana yin rajistar ɗalibai ba tare da kuɗin rajista ba, tare da manufar yaɗa ilimi da buɗe damar samun ilimi ga al’umma a Afrika da sauran ƙasashen duniya.
