Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin Samar da Zaman Lafiya na ƙasa, wanda tsohon Shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ke jagoranta, tare da Babban Limamin Cocin Katolika, Most Reɓ. Matthew Kukah, a matsayin mai gudanar da shi, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan siyasa kan yin kamfen mai ɗauke da kalaman tayar da hankali ko tunzura jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan rahoton samun wasu al’amura 60 da suka shafi zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar cikin wata guda, ciki har da rikicin siyasa, tsoratarwa, barazana, kai hari ko tarwatsa harkokin siyasa da kuma yaɗa bayanan ƙarya.
Kwamitin ya bayyana matsayinsa ne a cikin wata sanarwa da Abdulsalami Abubakar da Matthew Kukah suka sanya wa hannu tare a ranar Litinin.
A cikin sanarwar, kwamitin ya buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su gaggauta dakatar da yaɗa bayanan ƙarya, kalaman tunzura jama’a ko duk wani saƙon da zai iya haddasa rikici. Ya kuma buƙace su da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya, tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, tare da hana magoya bayansu shiga harkokin da suka saɓa wa doka, tsoratar da jama’a ko kawo cikas ga harkokin siyasa.
Kwamitin ya ce yayin da tsarin zaɓen 2027 ke ci gaba, matsayinsa a fili yake cewa dole ne kowane ɗan takara ya samu damar gudanar da kamfen cikin zaman lafiya, kowace jam’iyyar siyasa ta samu damar gudanar da harkokinta bisa doka, sannan kowane ɗan ƙasa ya samu damar zaɓar ɗan takarar da yake so ba tare da tsoratarwa ko tilastawa ba.
Kwamitin ya kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, INEC, da ta ƙara ƙarfafa sa ido kan harkokin kamfen na siyasa tare da tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta shekarar 2026 da sauran ƙa’idojin da suka shafi jam’iyyun siyasa da yadda ya kamata a gudanar da kamfen.
Ya ce idan aka samu wani ɓangare ya karya dokokin da suka shafi zaɓe, ya kamata INEC ta ɗauki matakin da ya dace a cikin ikon da doka ta ba ta, tare da tura duk wani laifi da ake zargin ya shafi aikata laifi ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.
Kwamitin ya kuma buƙaci hukumomin tsaro, musamman Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, da su ƙara kaimi wajen gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da kuma bisa hujjoji kan laifukan zaɓe da rikicin siyasa.
Kwamitin ya tunatar da dukkan waɗanda suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa cewa yarjejeniyar alƙawari ce mai muhimmanci da aka yi wa jama’a, ba wai wata sanarwa ce ta bikin kawai ba.
Gargadin ya zo ne kimanin makonni shida bayan manyan jam’iyyun siyasa da ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa ta farko da aka shirya domin tsarin zaɓen shekarar 2027, inda suka yi alƙawarin guje wa tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa bayanan ƙarya, kai wa abokan hamayya hari da kuma duk wani hali da zai iya kawo cikas ga zaɓe.
Kwamitin ya bayyana cewa cibiyarsa mai lura da tsaro da harkokin zaɓe ta bibiyi abubuwan da suka shafi harkokin siyasa tsakanin ranar 19 ga Agusta zuwa 19 ga Satumba, inda ta gano al’amura 60 da suka shafi zaɓe. Wasu daga cikin waɗannan al’amura sun saɓa wa alƙawuran da aka yi a ƙarƙashin Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa.
Bayanan ƙarya da yaɗa bayanan ƙarya ne suka kasance mafi yawa daga cikin abubuwan da aka gano, inda aka samu irin waɗannan al’amura guda 24, waɗanda suka kai kashi 40 cikin 100 na jimillar al’amuran da aka samu.
Bayan haka kuma, an samu hare-hare da tarwatsa harkokin siyasa da kadarorin da suka shafi siyasa guda 13, wanda ya kai kashi 21.7 cikin 100. Haka kuma an samu al’amuran tsoratarwa da barazana ga ’yan siyasa guda 10, ciki har da wasu da suka shafi jami’an tsaro, wanda ya kai kashi 16.7 cikin 100.
An kuma samu al’amuran tashin hankalin siyasa da daba guda shida, wanda ya kai kashi 10 cikin 100, yayin da kalaman tunzura jama’a suka kai guda huɗu, wato kashi 6.7 cikin 100.
Kwamitin ya kuma ce an samu wani lamari guda da ya shafi takaita ’yancin faɗar albarkacin baki, wani guda da ya shafi rikicin cikin gida na jam’iyya, da kuma wani guda da ya shafi ƙoƙarin sayen ƙuri’un jama’a.
Kwamitin ya ce waɗannan alkaluma sun nuna yadda ’yan siyasa da magoya bayansu ke karkata daga tsarin gudanar da kamfen cikin zaman lafiya da kuma mayar da hankali kan manufofi, wanda shi ne abin da Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa ta tanada.
Ya yi gargadin cewa irin waɗannan abubuwa na iya hana wasu jama’a shiga harkokin siyasa, rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe, tare da ƙara tsananta rikice-rikicen siyasa yayin da fafatawar neman mulki ke ƙara ƙarfi.
An ƙaddamar da cibiyar lura da tsaro da harkokin zaɓe a Abuja a ranar 14 ga Oktoba, 2025, tare da haɗin gwiwar Tarayyar Turai ta hanyar shirinta na tallafawa shugabanci na dimokuraɗiyya a Nijeriya. Manufar cibiyar ita ce bibiyar, nazari da kuma mayar da martani kan barazanar da za ta iya tasowa dangane da zaɓe.
Sabon gargadin na kwamitin ya biyo bayan sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa da aka gudanar a ranar 18 ga Agusta, inda manyan jam’iyyun siyasa da ’yan takara suka yi alƙawarin gudanar da kamfen bisa manufofi da kuma kauce wa tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa bayanan ƙarya, kai wa mutane hari da kuma duk wani hali da zai iya lalata tsarin zaɓe.
Taron sanya hannu kan yarjejeniyar, wanda Kwamitin Samar da Zaman Lafiya na ƙasa ya shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kukah, ya samu halartar Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa, Farfesa Joash Amupitan; shugabannin jam’iyyun siyasa; ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya; Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu; da kuma wasu jami’an diflomasiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilta; ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Nigerian Democratic Congress, Peter Obi; ɗan takarar Jam’iyyar Social Democratic Party, Adewole Adebayo; da ɗan takarar Jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, na daga cikin waɗanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar.
Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar African Democratic Congress, da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Allied Peoples’ Moɓement, ba su halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ba.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya kuma yi gargadin cewa ana samun abin da ya kira “ƙara dawowar kalaman ƙiyayya cikin mummunan yanayi”, tare da yaɗuwar rarrabuwar kawuna mai guba, shirya yaɗa bayanan ƙarya da kuma siyasar da ta fi mayar da hankali kan mutum maimakon manufofi.
Ya ce wannan lamari na ƙara tayar da hankali musamman ganin yadda Nijeriya ke gabatowa babban zaɓen da ake sa ran zai kasance cikin zaɓukan da za su fi fuskantar gagarumar fafatawa tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.
