
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADP a Jihar Filato, ta sake jaddada matsayarta cewa wajibi ne Sanata Pam Mwadkon Dachungyang ya bar kujerar Sanatan ta yankin Filato ta Arewa a nan take sakamakon ficewar da ya yi daga cikin jam’iyyar.
ADP ta kuma bayyana ikirarin cewa akwai rikici a cikin jam’iyyar a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a da ba shi da tushe a tsarin mulki.
A sanarwar da shugabancinta na ƙasa ya fitar a ranar Juma’a, ADP ta ce matsayin nata ya ta’allaka ne akan kundin tsarin mulkin ƙasa da aka yi wa gyara, wanda ya tanadin cewa duk ɗan majalisar da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar siyasa dole ne ya rasa kujerarsa idan ya sauya sheƙa, sai dai idan ficewar ta samo asali ne daga rabuwar kai ko haɗewar jam’iyyar da ta ɗauke shi takara.
A cewarta, “Babu wata rabuwar kai, haɗewa, ko ɓangare-ɓangare a cikin Jam’iyyar Action Democratic Party, ko a matakin ƙasa ko a matakin jiha. Ficewar Sanatan ta kasance ta son ransa, kuma ya amince da hakan da kansa, don haka bai faɗa cikin keɓantaccen tanadin da kundin tsarin mulki ya amince da shi ba.”
ADP ta lura cewa rubutacciyar sanarwar Sanatan da kansa wadda ya bayyana cewa ba mamba ba ne a jam’iyyar ta ƙara tabbatar da wajibcin doka na miƙa
wuya da barin kujerar da ya samu a ƙarƙashin tutar ADP a zaɓen Sanata na ranar 3 ga Fabrairu, 2024.
Kazalika, ta yi watsi da duk wani yunƙuri na dogaro da zargin rikice-rikicen cikin gida a matsayin hujjar riƙe kujerar, tana mai cewa hakan ba shi da tushe a doka.
“Matsalolin gudanarwa na cikin jam’iyya—ko da kuwa na gaske ne ko na ƙirƙira—ba su rinjayi Kundin Tsarin Mulki ba. Ba za a iya amfani da su a matsayin garkuwa don kauce wa sakamakon sauya sheƙar siyasa ba”, inji sanarwar.
