Ayyukan raya ƙasa da gwamna ke aiwatarwa suka sa na shiga APC – Dr Aminu Waziri

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsohon babban sakatare a gwamnatin Masari Dr Aminu Waziri Malumfashi ya faɗa haka a wata hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce da shi aka kafa jam’iyar haɗaka ta ADC a jihar Katsina amma da tafiya tayi tafi sai ya lura cewa bata kai ƙarfin da za ta ƙalubalanci jam’iyar APC ba wanda ita take da gwamnati.

Dr waziri Malumfashi wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Katsina ya ƙara bada wasu dalilai da suka sa ya bar jam’iyar adawar ta ADC a Katsina.

Wasu daga ciki kuwa sun haɗa da tsari na cigaban al’umma na tsawon shekara biyar wanda nan gaba za a sha domin dimokraɗiyya,ya ce.

“Sabunta birane da bunƙasa ilimi, tsaro, aikin noma da bunƙasa sana’o’i da biyan ma’aikata da suka ajiye aiki kudin su na Gratuty wanda hakan ya sanya shi zama Gwamna da yafi kowa a jihohin Arewacin ƙasar wajen gudanar da ayyukan bunƙasa ƙasa,”Dr waziri ya ce.

Ya bayyana yadda Dikko Raɗɗa ya aiwatar da kasafin kuɗin shekarar da ta wuce har zuwa 85 bisa 100 da ya ce ko a jarabawa ne a makaranta ka ci wannan kaso to ka janye inji shi.

“Kan waɗannan aikace-aikace na raya ƙasa da Malam Dikko Raɗɗa ya aiwatar ya sanya ni na yanke shawarar shiga jam’iyar APC domin cigaban jihar,”Dr Aminu Waziri ya ce.

Yayi magana akan yanayi tsaro a jihar inda ya bayyana cewa shima Gwamna Dikko Raɗɗa ya gaji rashin tsaro bayan da ya amshi mulkin jihar, sai ya yaba masa kan matakan da yake ɗauka na kawo zaman lafiya.

Tsohon babban sakataren wanda ya ce ya riga ya yi rajista kuma ya amshi katin zama ɗan jam’iyar APC “kuma zan taimakawa gwamna Dikko Raɗɗa wajen samun nasarar ciyar da jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya

By ukarofi