Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa mata ‘yan kasuwa da Naira miliyan 500

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa mata, inda ya bayyana taron “Where Influence Meets Investment” a matsayin muhimmin dandali na bunƙasa tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.

Da yake jawabi a babban taron Katsina Inner Wheel Development Initiative (KIWDI), wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar ma’aikatar harkokin mata, Gwamna Raɗɗa ya ce taron ya samar da muhimmiyar dama ga shugabannin mata, ’yan kasuwa, masu zuba jari da abokan hulɗar ci gaba domin bincika hanyoyi masu amfani na ƙarfafa tattalin arziki, bunƙasa jagoranci da koyon sana’o’i.

“Na zaɓi in zo in kuma zauna har ƙarshen wannan shiri ne saboda duk wani shiri da ya shafi ci gaban mata ya cancanci cikakkiyar kulawa da goyon bayana.

Bunƙasa mata, a sauƙaƙe, bunƙasa al’umma ne,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina za ta ƙara ware Naira miliyan 500 musamman domin tallafa wa ’yan kasuwar mata a faɗin jihar, da nufin haɓaka ƙwarewa, faɗaɗa kasuwanci da samar da hanyoyin dogaro da kai masu ɗorewa.
“Ku tabbata a yau ina tsaye tare da ku, kuma gwamnatina za ta ci gaba da tallafa wa dukkan shirye-shiryen da ke ƙarfafa mata a Jihar Katsina,” in ji shi.

Malam Dikko Raɗɗa ya jaddada cewa taron ya wuce zama taro kawai, yana mai bayyana shi a matsayin wata sanarwa mai ƙarfi ta haɗa jarin tattalin arziki da tasirin jagoranci. “Tasiri ba tare da jari ba wahayi ne ba tare da sakamako ba. Jari ba tare da tasiri ba kuɗi ne ba tare da tausayi ba. Amma idan tasiri da jari suka haɗu, tattalin arziki yana bunƙasa, al’umma sukan zama masu adalci, ƙasashe kuma sukan ɗaukaka,” in ji Dikko.

Da yake haskaka muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen ci gaban al’umma, Gwamnan ya ce: “Duk al’umma da ke tauye mata tana rage damar da take da ita.

Duk tattalin arzikin da ke ware mata yana raunana yawan amfaninsa. Kuma duk jagorancin da ya gaza ƙarfafa mata yana raunana tubalinsa na zaman lafiya, ƙirƙire-ƙirƙire, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.”

Kan gudummawar mata ga kasuwanci da ci gaban al’umma, Gwamna Raɗɗa ya ce mata su ne ginshiƙin kwanciyar hankali na tattalin arziki da zamantakewa. “Mata na jagorantar kasuwanci, na kula da iyalai, na ƙarfafa al’umma, kuma na gina al’ummomin gobe. Sai dai sau da yawa tasirinsu bai yi daidai da damar samun jari, kasuwanni, dama da wuraren yanke shawara ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma nuna ƙoƙarin Jihar Katsina na ƙara wakilcin mata a harkokin mulki, ciki har da naɗin mata a majalisar zartarwar jihar.

“Idan mata sun bunƙasa, gidaje sukan wadata. Idan mata sun gina kasuwanci, ayyukan yi sukan ƙaru. Idan mata suka jagoranci al’umma, sukan zama masu haɗa kowa, masu kwanciyar hankali da masu hangen nesa,” in ji shi.

Ya kuma lissafa nasarorin baya-bayan nan na gwamnatinsa, inda ya ce an ƙarfafa mata sama da 14,000 a makon da ya gabata, an tallafa wa ’yan mata matasa 1,000 makonni biyu da suka wuce, yayin da fiye da mata 36,000 suka amfana da shirye-shiryen ƙarfafawa daban-daban a bara.

“Dole ne jari ya kasance da manufa, kuma saka hannun jari ya zama na haɗa kowa da kowa. Bankuna da cibiyoyin kuɗi su ƙirƙiri hanyoyi da gangan domin bai wa mata na gida damar samun kuɗaɗe cikin mutunci da sauƙi,” in ji Gwamnan, ya ƙara da cewa Jihar Katsina ta zuba sama da Naira biliyan 4 a shirin mata na Najeriya (Nigerian Women Project).

Da yake jawabi ga shugabannin mata da matasan mata a jihar, Gwamna Raɗɗa ya ce: “Ga shugabannin mata da ’yan kasuwa, muryarku, hangen nesanku da ƙimarku suna da muhimmanci. Ga matasan mata a faɗin Jihar Katsina, makomarku ba a dakatar da ita ba.

Ba sai kun nemi izini don shiri ba, kuma ba sai an tabbatar muku kafin ku jagoranci ba.”

Ya kammala da jaddada muhimmancin aiki fiye da magana. “Tarihi ba zai auna mu da jawabanmu ba, sai da tsarin da muka gina, rayukan da muka ɗaga, da jarumtar da muka nuna a lokutan da suka fi muhimmanci. Tare, za mu iya gina makoma inda tunani ya koma jari, tasiri ya zama sakamako, kuma Jihar Katsina ta zama abin koyi na ci gaba mai haɗa kowa da wadata ta bai ɗaya,” in ji shi.

A jawabinta na maraba, Hajiya Amina Zayyana, wadda ta kafa Katsina Inner Wheel Development Initiative (KIWDI), ta ce taron ya sanya mata a matsayin masu zuba jari, ’yan kasuwa, masu ƙirƙire-ƙirƙire da masu warware matsaloli. “Idan kasuwancin mata ya bunƙasa, iyalai sukan samu kwanciyar hankali, al’umma sukan bunƙasa, jiha kuma ta wadata,” in ji ta.
Ta bayyana cewa taron na haɗa mata da damammaki, tsare-tsaren tallafi da muhimman albarkatu.

“Wannan ya wuce ƙarfafawa kawai; ya shafi horaswa, shigar da mata cikin harkokin dijital, damar shiga kasuwa da tallafi na tsari,” in ji ta.

Kwamishiniyar harkokin mata, Hon. Aisha Aminu Malumfashi, ta yaba wa masu shirya taron tare da jaddada ƙudurin gwamnati na aiwatar da shirye-shiryen ƙarfafa mata masu tsari da sakamako.

Ta ambaci manyan shirye-shirye kamar Women Affinity Groups (WAGs) a dukkan ƙananan hukumomi, damar samun tallafin MSME, da ci gaba da shirye-shiryen haɓaka ƙwarewa.

Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Alkali Usman Baba, ya bayyana ƙarfafa mata a matsayin larura a harkokin mulki.

“Al’ummomin da ke ware mata suna raunana ɗabi’arsu, cibiyoyinsu da damar ci gabansu,” in ji shi, yana mai yaba wa Jihar Katsina kan tsarinta na haɗa kowa da kowa.

Taron ya samu halartar wakilan hukumomin tarayya, darakta hanar na hukumar bunƙasa yawon buɗe ido ta Najeriya, Dr. Olayiwola Awakan; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma Shugaban Majalisar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina, Sanata Hadi Sirika; Shugaban Kamfanin KB Lamah Motors, Kabir Lamah Malumfashi; mambobin Majalisar Zartarwar Jihar Katsina; shugabannin kasuwanci; ’yan kasuwar mata; da abokan hulɗar ci gaba.

By ukarofi