‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mai shayarwa da mutane da dama a harin ƙauyukan Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga a wani karon, sun sake kai farmaki a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja, inda suka ƙone ofishin ‘yan sanda da coci, sannan daga bisani suka yi garkuwa da mai shayarwa da ‘ya’yanta huɗu da kuma wasu mutane da ba a kai ga sanin adadinsu ba.

An ruwaito cewa, sun kuma halaka wata tsohuwa a yankin Kabe, inda kuma suka yi awon-gaba da kayan abinci masu yawa a harin wanda suka ƙaddamar a safiyar ranar Lahadi.

Haka kuma an gano cewa cocin da suka ƙona na Ɗarikar ‘United Missionary Church of Africa’ (UMCA) ne.

A cewar wani mazaunin yankin, ‘yan bindigar sun bar garin da misalin ƙarfe 6 na safe inda suka nufi wani ƙauye mai suna Sokonbara da ke kusa da Kabe, inda aka ƙaddamar da ɗaya harin.

Kazalika, an gano cewa wani Shugaban makarantar firamare kuma tsohon shugaban ƙungiyar malamai (NUT), Malam Ahmed Burade tare da matarsa da ‘ya’yansu biyar na daga cikin waɗanda ‘yan bindigar suka ɗauke.

Saidai, hidimastan ya samu damar tserewa a lokacin da ake ba-takashi tsakanin masu garkuwar da ‘yan bijilante.

Al’umma a ƙauyukan jihohin Neja da Kaduna na fuskantar matsalolin hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, Rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba a hukumance akan al’amarin.

By Babaji