
Daga BELLO A. BABAJI
A yayin da aka sake samun wasu hare-hare a yankunan Zikke da Kimakpa a Ƙaramar Hukumar Bassa dake Filato, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar ya shirya taron tsaro na gaggawa don warware matsalolin tsaro a yankunan.
An gudanar da zaman ne a yammacin ranar Litinin a Gidan Gwamnatin jihar dake Jos, inda aka tattauna yadda za a dawo da zaman lafiya ta hanyar ɗaukar matakan kariya ga hare-haren da ke faruwa akai-akai.
Ya ce, sama da ƴan bindiga 100 suka farmaki mutane a yankunansu da asubahin Litinin, lamarin da ya sabbaba mutuwar mutane 51 da ƙone gidaje da dama.
Sarkin garin Kwall, wakili Tongwe ya ce maharan sun shigo ƙauyen ne cikin tsakar dare a yayin da suka tafi sintiri a wasu wurare, inda bayan harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi ne aka rasa mutane da dama ciki har da ƙananan yara.
Tuni Sufeton ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya umarci a baza jami’a na musamman zuwa yankunan da ke fama da hare-haren don shawo kan al’amarin.
