Firaministan Habasha ya ƙaddamar da ɗakin adana kayan kimiyya da fasaha da ƙasar Sin ta samar

Daga CMG HAUSA

Firaministan ƙasar Habasha Abiy Ahmed, ya ƙaddamar da wani katafaren gidan adana kayan kimiyya da fasaha da ƙasar Sin ta samar, a Addis Ababa, babban birnin ƙasar.

Gidan adana kayan kimiyya da fasaha na Afirka mai shiffar Kubba, ya zama wani dandali da za a iya tunani a kuma ƙirƙiro sabbin fasahohi na kimiyya, don tallafawa ci gaban ƙasar Habasha.

Yana mai cewa, gidan zai taka muhimmiyar rawa wajen canja ƙasar Habasha zuwa tsarin tattalin arziki na zamani.

A wani ɓangare na bikin ƙaddamar da gidan, ƙasar dake gabashin Afirka, ta kuma karɓi bakuncin taron kwaikwayon tunanin ɗan Adam na Afirka irinsa na farko.

Taron ya hallara masu bincike a ɓangaren kwaikwayon tunanin ɗan Adam, da masana kimiyyar lissafi da injiniyoyi, da ‘yan kasuwa da sauransu, domin tattauna dabarun da ƙasashen ke da su game da samun ci gaba mai ɗorewa, ta hanyar amfani da fasahar kwaikwayon tunanin ɗan Adam, ta hanyar musayar ƙwararru a fannin ilimi da aikace-aikace a sassa masu tarin yawa, kamar aikin gona, kiwon lafiya, harkokin kuɗi, ɓangaren samar da hidima, tsarin bayanai na yanki, da tsaron intanet da masana’antun samar da kayayyaki.

Babban darektan cibiyar fasahar kwaikwayon tunain ɗan Adam ta ƙasar Habasha Worku Gachena, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ƙasar Sin ba kawai tana taimakawa ƙasar Habasha wajen samun irin wannan katafaren gidan adana kayan kimiyya da fasaha na zamani ba, har ma tana kara bai wa ƙwararrun ƙasar Habasha kwarin gwiwa game da fasahar kwaikwayon tunanin ɗan Adam.

Mai fassara: Ibrahim