Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas tare da dakatar da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida. Wannan mataki ya biyo bayan rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar, wanda ya haifar da rashin daidaito tsakanin gwamna da ‘yan majalisar jihar.
A wata sanarwa da gwamna Fubara ya fitar ranar Laraba, 19 ga Maris, 2025, ya yi kira ga al’ummar Jihar Ribas da su kasance masu bin doka da oda tare da kwantar da hankalinsu. Ya ce tun bayan hawansa mulki, dukkan matakan da yake ɗauka suna bisa ƙa’ida da bin kundin tsarin mulkin ƙasa. Ya kuma jaddada cewa ya ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Fubara ya bayyana cewa, duk da rikicin siyasa da ake fuskanta, gwamnatinsa ta ci gaba da gudanar da ayyuka masu muhimmanci, ciki har da biyan albashi da kuma aiwatar da manyan ayyuka domin ci gaban jihar. Ya kuma ce bayan hawan mulkinsa, ya tabbatar da dawowar kwamishinonin da suka yi murabus a baya, domin tabbatar da haɗin kai da ci gaba.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙasa Tinubu ya bayyana cewa matakin na dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa, tare da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar, na da nufin dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar. An naɗa tsohon babban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ette Ibas mai ritaya, a matsayin mai kula da jihar don tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki cikin lumana.