Garba Shehu: Murucin kan dutse

Daga KWAMARED IBRAHIM ABDU ZANGO

Gaskiyar lamari na yaba da ƙwazon Malam Garba Shehu wanda yanzu yake mataimaki na musamman ga fadar shugaban ƙasa malam Muhammadu Buhari a matsayin mai watsa labarai na musamman wato dai a hausance, mai yaɗa labarai wanda idan ka ji shi to da izinin shugaban ƙasar ya yi.

Malam Garba Shehu ba shi kaɗai ba ne akwai wani shahararren ɗan jarida shi ne mai faɗin wasu abubuwa wanda suka danganci ƙasashen waje shi ma dai da ka ji shi, to da yawun shugaban ƙasa ya yi, wato shi ne, Mista Adeshina.

Gaskiya a duk masu taimaka wa fadar shugabannin ƙasar Nijeriya in banda Malam Abba Dabo wato sakataren yaɗa labarai na shugaba marigayi Alhaji Shehu Shagari 1979-1984, do wuya a samu masu kyakkyawan yanayi, irin nasu Malam Garba Shehu da Mista Adesina.

Shi Malam Garba Shehu ɗan jarida ne na gidi kuma ya riqe muƙamai da yawa kusan na sanshi amma daga nesa lokacin da ya yi Manajan Darakta na Gidan Jaridar Triumph ta jihar Kano, kuma an ce ya tava zama editan jaridar New Nigeria dake Kaduna, wadda abin kaico tun kusan shekarar 2007 aka rufe gidan har kuwa zuwa wannan shekara ta 2022, gashi kuma cikin ikon Allah da fatan zamu shiga sabuwar shekara ta 2023 cikin ‘yan kwanaki ƙalilan.

Gaskiya da ba don samun Daily Trust sun ceto masu buƙatar Hausa ba ta buga jaridar Hausa wato Aminiya da kuma kamfanin Triumph na jihar Kano dake buga Albishir, sai jaridar Leadership Hausa da kuma Manhaja da sai muce Inna-Lillahi, domin an kashe mana buƙatar bunƙasa harshen Hausa.

To su Malam Garba Shehu Ahuwonku kafin abubuwa su cakuɗe kamata yayi ku shawarci Gwamnonin Arewa kafin su tafi su nemo hanyar gyara New Nigerian Newspaper don ƙarin daraja ga waɗannan jaridu masu zaman kansu, Malam Garba Shehu, ‘yan Nijeriya kususan ‘yan Arewa suna kaico da cewa Shugaba Buhari ya ba wa ‘yan arewa da yawa muƙamai amma komai ya ɓalɓalce kususan na kyautata wa Arewa. Jama’a da yawa suna mamakin yadda aka haihu a ragaya!

Gaskiya ne mutane sun kwana da ganin kamar duk da qaunar da suka yi wa Shugaba Buhari na sadaukar da rayuwarsu wurin zaɓensa kamar bai yi komai ba, ba don komai ba, saboda ba su san cewa mutanen da ya kawo ya ba su muƙamai su ne suka ƙi taɓuka komai ba shi ba.

Hakazalika, an yi aiki sosai amma ‘yan ta’adda sun hana a ga ayyukan da aka yi ko ake yi saboda rikice-rikicen babu gaira babu dalili kusan a rabin jihohin Nijeriya kowa ya san cewa tun 1981 – 1985 – 1995 ake samun turjiya daga gabashi Nijeriya zuwa kusurwar Neja-Delta; kowa ya san ɓarayin man fetur tun lokacin sojiji suna mulki ba su magance waɗannan tsageru ba shekara da shekaru.

Sai kuma masu neman ƙasar Oduduwa da ‘yan Biafra, waɗannan ƙungiyoyin tsagerun sun daɗe suna cin karensu babu babbaka, ba a iya ci musu ba, kususan ‘yan NEJA-DELTA sai gwamnatin marigayi Yar’adua kaɗai ta shawo kansu kuma daga ƙarshe suka sake kunga Arewa! To kwatsam sai ga Boko Haram, asalin abin rikici ne da gwamnatin Borno lokacin wani mashahurin mai kuɗi kuma gwamna, bayan wannan sai satar shanu a Arewa maso yamma, Katsina, Sokoto, Zamfara da wani jiƙon Kebbi, ɗauki kuma wurare kamar Kaduna da Neja abin akwai abin takaici ƙwarai, domin duk wanda bai shiga wuyar da waɗannan jihohi suke ciki, shi a wurinsa gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi aiki ba!

To Malam Garba Shehu aiki na nan gaba domin akwai kekecin cewa wannan abubuwan ta’ajibi ba zai ƙare ba idan ‘yan Nijeriya ba su daina tsegumi da tsinuwa ga ƙasarsu ba. Nasan akwai ƙasashe masu yawa da suke cikin matsi fiye da Nijeriya kodayake kowa nasa ya sani, amma duba da cewa duk ɗan’adam ɗaya yake, duk mai sauraren kafofin yaɗa labarai zai ji da gani a talabijin yaƙe-yaƙe a wurare kamar Yemen, Somaliya, Habasha, Sudan ta Kudu, Kongo, Mali, Burkina Faso da dai wurare irin su Siriya da Mali waɗannan qasashe sun shiga shekara da shekaru a nata faman yaqi kuma Allah ne kaɗai ya san lokacin ƙarewarsa saboda haka nake ganin ‘yan Nijeriya mu cigaba da addu’a har Allah ya kawo ƙarshen waɗannan masifu a Nijeriya.

Duk inda ake waɗannan alkaba’i akwai wasu a waje a ɓoye masu ingiza ababen kuma wata masu bincke sun san da haka sai dai wataƙil abin ya fi ƙarfinsu ko kuma dai ana jiran lokaci ne kurum.

Malam Garba Shehu muna alfahari da kai ƙwarai da gaske domin mun san kai ɗan jarida ne kai na gidi kuma mai ƙaunar Nijeriya, sai nake sha’awar cewa ka shawarci wasu daga cikin gwamnoninmu kususan na Arewa ta yamma, suyi ƙoƙari kafin su tafi su farfaɗo da New Nigerian Newspaper duk da cewa Daily Trust, Blueprint, Triumph da sauransu na ƙoƙari sosai-sosai!

Haka ina godewa dukkan ‘yan jaridar Arewa, har da su manyan ‘yan jaridu irinsu, Halilu Ahmad Getso, Malam Muhammadu Garba Kamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, da Sani Zoro. Malam Garba Shehu, gaisuwa ta musamman ga Ministan yaɗa labarai Lai Muhammad saboda kare mutuncin Nijeriya da Afrika.

Hakaza, ina miqa gaisuwa ga Mamallakan jaridar Daily Trust, Aminci, Manhaja ta Blueprint da Albishir ta Triumph. Ina kira ga ‘yan Nijeriya cewa Allah Ya zaɓa mana shugabannin adalai to haka yake amma kamata yayi muma mu zama adalai.

Domin shugabannin nan a cikinmu suke domin duk mun san inda suka fito ɗauki marigayi Murtala ɗan Kano ne kuma haifaffen unguwar Kurawa a cikin birnin Kano, haka marigayi Shugaba Abacha ɗan Kano ne kuma haifaffen Fagge ta birnin Kano, ɗauki General Gowon ɗan birnin Zaria ne ta Kaduna, kuma ɗan kabilar Angas ta Plateau.

Haka Janar Babangida da Abdussalami Abubakar ‘yan Minna jihar Neja; marigayi Umaru Musa Yar’adua, ɗan birnin Katsina ne haka marigayi Shehu Shagari ɗan Sokoto ne, kuma haifaffen Shagari, yaya Obasanjo ɗan Abeokuta ne kuma ɗan qauyen Otta, sai Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ɗan Bayelsa kuma ɗan ƙauyen Otoki kuma malamin makaranta.

To ashe dai ba daga wata ƙasa suka zo ba, daga cikinmu suke. Saboda haka, mu ma mu zama adalai kafin cewa shugaba ya zama adali. Kuma Nijeriya tana fama da ma’aikata wasu ba sa tunanin Nijeriya illa kansu kamar dai wasu da shugaba Buhari ya naɗa amma suka naɗe hannuwansu daga su sai ‘ya’yansu sai matayensu!

Allah Ya tsare, Amin.

Kwamared Ibrahim Abdu Zango
Kano, Nijeria, 08175472298

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *