Daga WAKILINMU a Sakkwato
Kwamitin mai da alkhairi da alkhairi na Gidauniyar tsohon gwamnan Jihar Sakkwato da haɗin gwiwar cibiyar yaɗa addinin Musulunci ta IET sun gudanar da taron bita na yini biyu ga ɗalibai game da fasahar gina kai, dogaro da kai, kyakkyawan amfani da lokaci, fasahar amfani da dukiya, hulɗa tsakanin ƙungiyoyin haɗin kai, da shiga ayyukan waƙafi, da sauran su.
Shugaban kwamitin Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ya bayyana cewa, an shirya taron ne domin ƙara horar da ɗalibai don su ƙara zama masu amfani ga al’umma, kuma kansu ya ƙara wayewa tun suna ƙanana. Ya ƙara da cewa, ayyukan Kwamitin ba sun tsaya ne kawai ga batun raya ilimi, raba abinci, da inganta kiwon lafiya, da ayyukan jinƙai ga al’umma, kawai ba, har ma da kyautata halaye da inganta tunani ga manyan gobe.
Shugaban ya yi godiya ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa kan damar da ya bayar ta yin aikin. Sannan ya yi godiya ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da Majallisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Cibiyar IET da ilahirin mambobin Kwamitin.
A nasa jawabin, Sakataren Kwamitin Hon. Sagir Bafarawa ya bada tabbacin cewa, da irin waɗannan ayyuka na faɗakarwa da ake shiryawa za a samu al’ummar da za su kawo sauyi a dukkan ɓangarorin rayuwa, musamman duba da yadda aka zaƙulo ɗaliban da irin hazaƙar su. Ýa kuma yi fatan su ma ɗaliban za su zama masu amfani ga al’ummar da suka fito.
Hon. Sagir ya ƙara jaddada yadda Kwamitin ya bai wa sha’anin ilimi muhimmanci, yayin da a cewarsa tun yanzu ma kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.
Hon. Shehu Balarabe da shi ma ya samu halartar taron ya yi kira ga ɗaliban da su dage ga sha’anin karatun su, domin su ma su taimaki wasu nan gaba.
Wasu ɗaliban da suka halarci taron bitar sun yi godiya ga tsohon Gwamna Bafarawa, Cibiyar IET da Kwamitin Maida Alheri da Alheri.
An ba da takardun shaidar halartar taron bitar ga ɗaliban da suka halarta.
