Gidauniyar C&C Friends ta yi jimamin gobarar kasuwar Singa ta Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidauniyar C&C Friends, ta yi jimamin gobarar da ta auku a kasuwar Singa da ke Jihar Kano ranar Assabar, wadda ta yi sanadiyyar ƙonewar wani babban sashenta.

A wata sanarwa daga Shugaban gidauniyar kuma wanda ya samar da ita, Sanusi Garba Kalambaina, C&C Friends ta bayyana alhininta game da asarar da aka tafka a iftila’in, wanda ya lanƙwame kayayyaki na biliyoyin nairori, kamar yadda rahotanni suka nuna.

A safiyar ranar Asabar ne al’amarin ya auku a wani sashen kasuwar, wadda ɗaya ce daga cikin manyan kasuwannin abinci a Nijeriya, inda har zuwa Lahadi duk da hoɓɓasa na jami’an kashe gobara da wasu masu bayar da agajin gaggawa, gobarar ta cigaba da ci.

A cewar gidauniyar, irin wannan asarar da ta auku musamman ga ƙananan ‘yan kasuwa da suka tara dukiyoyinsu bisa aiki tuƙuru, abu ne mai raɗaɗin gaske, lamarin da ya haifar da cikas ga harkokin kasuwanci a jihar.

Ta kuma aika saƙon jajenta ga waɗanda al’amarin ya shafa a madadinta da Kamfanin Sagarka Security Services da Garba Kalambaina Nijeriya Limited da fatan Allah ya mayar musu da mafi alheri.

By Babaji