Shettima zai jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya a jajen gobarar Singa yayin da Tinubu ya umarci a yi bincike

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci a yi cikakken bincike a game da aukuwar gobara akai-akai a kasuwar Singa da ke Jihar Kano bayan da aka sake samun wata da ta lanƙwame biliyoyin nairorin kayayyaki.

Haka kuma shugaban ƙasar ya Umar Mataimakinsa Kashin Shettima da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa jihar domin jajenta wa waɗanda iftila’in ya afka wa da bayar da tallafi a gare su.

Gobarar, wadda ta auku a yammacin ranar Asabar, ta cigaba da ci da lalata dukiyoyi a kasuwar har zuwa saniyar Lahadi.

Kasuwar Singa ɗaya ce daga cikin manyan kasuwannin abinci a Nijeriya.

Wannan al’amari ya faru ne a ƙasa da mako biyu da makamancinsa ya auku a wani sashen kasuwar, wadda ta babbake shaguna da wasu kadarori masu yawa.

Shugaba Tinubu ya bayyana al’amarin a matsayin abin tausayi da ya jefa mutane da dama cikin ƙunci musamman ganin yadda aka samu faruwar irin haka a lokuta mabanbanta kuma a waje guda.

A wata hirar wayar hannu da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar, Tinubu ya nemi da gudanar da bincike akan al’amarin gami da jajenta wa al’ummar jihar, kamar yadda Kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda.

By Babaji