Gidauniyar IDDEF ta yi taron yaye yaran da ta yi wa kaciya

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Gidauniyar tallafa wa Musulmi da mabuƙata ta duniya (IDDEF), ta yi wani taron yaye yaran da ta yi musu kaciya su kimanin 450 bayan sun warke daga kaciyar da aka yi musu.

Taron wanda aka gudanar da shi a Ofishin Gidauniyar dake gidan Ladi Haladu a Kan titin Zaria a Kano ya samu halartar manyan mutane, cikin su har da Shugaban Gidauniyar na duniya Sheikh Muhammad Turan wanda ya zo daga ƙasar Turkiyya domin halartar taron.

Tun da farko da ya ke Jawabi a wajen, babban mai kula da gudanarwar Gidauniyar a Nijeriya, Malam Askiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara. Ya bayyana cewar, “shi wannan abu ba sabo ba ne, domin duk shekara muna gudanar da gangamin yi wa yara kaciya wanda a wannan shekara ma cikin ikon Allah mun samu damar gudanar da shi. Wanda mu kan yi kaciya ɗin kuma mu samar da magunguna da Yara za su yi amfani da shi har zuwa lokacin da za su warke, sannan mu kan samar musu da naman da za su ci wanda a lokacin idan an yi kaciyar sai a yanka shanu a raba musu naman, Kuma bayan sun warke sai mu yi taron yaye su kuma muna yi musu ɗinki na sabbin kaya da ɗan kuɗin da za su riƙe kamar yadda sauran yara masu gata suke samu kuma hakan ne zai samu tabbatar aikin da muka yi an samu nasara.”

Ya ci gaba da cewar, “a wannan shekarar ma dai ga shi mun taru domin a yaye masu kaciyar, sai dai wannan taron na bana ya fi na baya da aka saba yi. Domin a bana yaran su 450 ne don haka sun waluce na baya. Sannan kuma a wannan shekarar, mun samu baƙuncin Shugaban Gidauniyar IDDEF ɗin na duniya Sheikh Muhammad Turan wanda ya zo daga Turkiyya domin ganewa idon sa, don haka wannan taro muhimmi ne a gare mu.”

Shi ma da ya ke Jawabi a wajen Shugaban Gidauniyar IDDEF na duniya Sheikh Muhammad Turan, ya yaba wa shugabannin Gidauniyar na Nijeriya bisa ƙoƙarin da su ke yi, kuma ya ce zuwan da ya yi ya ƙara masa ilimi musamman haɗuwar da yaran da aka yi wa kaciyar, don haka ya yi kira a gare su da su dage da karatu a matsayin su na yara da za su zama manya a nan gaba.

Bayan kammala taron dai an kwashi yaran a manyan motoci in da aka kai su masallacin Khanzu in da Kabarin Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya ke domin yin ziyara da addu’o’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *