Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Gidauniyar Zakah da Waƙafi a Jihar Gombe ta ci gaba da aikin ta na kyautata rayuwar mabuƙata ta hanyar rabon tufafin Sallah ga yara marayu da mabuƙata guda 100. Wannan tallafi yana daga cikin al’adar gidauniyar na taimaka wa waɗanda suke cikin buƙata, musamman a lokutan bukukuwan Sallah.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban gidauniyar, Amir Abdullahi Abubakar Lamido, ya bayyana cewa, gidauniyar na tattara tsoffin tufafi daga hannun masu hannu da shuni, tana tsaftacewa sannan tana sake rabawa ga mabuƙata.
Sai dai wannan shekara, gidauniyar ta rungumi sabon tsari na sayan sababbin tufafi daga matan da suka kammala horo a shirye-shiryen koyon sana’o’in hannu na gidauniyar.
Waɗannan matasa, da suka samu ƙwarewa a sana’o’i kamar ɗinki, sarƙa (bead-making), da kuma ƙera takalma, sun sayar wa gidauniyar kayayyakin da suka ƙera, abin da ya haifar da tasiri biyu: na tallafa wa mabuƙata da kuma samar da kuɗaɗen shiga ga matasan da ake horarwa.
“Ina ganin wannan tsari ba wai kawai yana faranta ran marayu da mabuƙata ba, har ma yana ba wa matasan da muka koyar da sana’o’i damar samun tallafi da ƙarfafawa ta fuskar kuɗaɗe. Wannan hanya ce mai ɗorewa da za ta ci gaba da inganta al’umma,” in ji Lamido.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni su bada zakkar su ta hannun gidauniyar inda ya tabbatar musu cewa gudummawar su tana kai wa ga waɗanda suka fi cancanta.
Lamido ya kuma jaddada cewa masu bada gudummawa da dama sun nuna gamsuwa da yadda gidauniyar ke gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da tasiri.
Baya ga rabon tufafin Sallah, gidauniyar ta kuma tallafa wa mata guda 75 da jari na ₦15,000 kowannensu. Waɗannan mata sun samu horo kan yadda za su sarrafa kuɗin su da kyau, ciki har da tanadi na kaso ɗaya bisa uku na ribar su a cikin asusu na musamman na tsawon shekara guda don tallafawa kasuwancin su ya ɗore.
Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI), Saleh Ɗanburan, ya yaba wa gidauniyar bisa ƙoƙarin ta na taimakon al’umma tare da kira gare ta da ta ci gaba da tsayawa akan manufofin addinin Musulunci.
Fitaccen malamin addini, Bello Doma, ya yaba wa ayyukan gidauniyar tare da bayar da shawarar kafa bankin microfinance don bayar da rance marar riba.
A cewarsa, wannan shawara za ta samar da taimakon kuɗi ga mabukata ba tare da kunyatar su ko ƙin amincewa da buƙatun su ba.
Shirye-shiryen gidauniyar Zakah da Waƙaf na ƙirƙire-ƙirƙire da tasiri suna ci gaba da canza rayuwa, suna kuma ƙara wa al’umma fata da ƙarfin gwiwa a Gombe.
