Daga USMAN KAROFI
Hukumar Shari’ah ta Jihar Kano tare da haɗin guiwar ƙungiyar World Assembly of Muslim Youth (WAMY) sun shirya taron shan ruwa ga waɗanda suka karɓi addinin Musulunci. An gudanar da taron a ranar Lahadi, 23 ga watan Ramadan, a harabar hukumar ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban hukumar, Sheikh Ali Danabba. Wannan shiri ya kasance wani ɓangare na kyautata wa sabbin Musulmai da inganta jin daɗinsu cikin al’umma.
A yayin taron, Sheikh Ali Danabba ya bayyana cewa hukumar shari’ah ta ayyana ranar 15 ga Ramadan a matsayin ranar da za ta ci gaba da shirya shan ruwa ga sabbin Musulmai duk shekara. Haka kuma, ya miƙa godiya ga gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙungiyar WAMY bisa tallafin da suka bayar don tabbatar da nasarar shirin.
Wakilin shugaban ƙungiyar WAMY, Alhaji Sanusi, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda shirin ya gudana, yana mai jaddada cewa ƙungiyarsu na ci gaba da goyon bayan Musulunci da kuma jin daɗin musulmi a duk inda suke. Ɗaya daga cikin sabbin Musulman da suka ci gajiyar shirin, A’isha Suraj, ta bayyana farin cikinta da irin karramawar da ake yi musu, inda ta ce “Lalle addinin Musulunci addini ne mai daɗi.”
A nasa jawabin, shugaban hukumar shari’ah, Dr. Sani Ashir, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa waɗannan yara domin ƙarfafa su a addini. Haka kuma, Gwani Hadi, kwamishinan hukumar, ya buƙaci al’umma da su nemi aure a cikin waɗannan sabbin Musulmai, yana mai cewa babu irin kyawawan halaye da ake nema face a wannan hukuma. Ya kuma yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
