Girmama cikakken ’yanci da yankunan ƙasa, wajibi ne a kan kowacce kasa babba, ko ƙarama

Daga FA’IZA MUSTAPHA

A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a wannan wata, ƙasar Sin, bisa jagorancin wakilinta na dindindin, ta kira taro kan samar da tsarin tsaro da ya dace da yanayin da ake ciki da girmama cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe, domin samun yanayin tsaro mai ƙarƙo a duniya.

Haƙiƙa kiran wannan taron da Wakilin Sin Zhang Jun ya yi ta zo a daidai lokacin da ya dace, ganin yanayin ƙalubale da duniya take ciki da kuma yadda ake keta cikakken ’yancin ƙasashe da takalar fada da kuma ingiza tayar da rikici.

Zamanin mulkin mallaka da danniya ko cinikin bayi ya wuce.

Ana cikin wani sabon zamani da ake neman ci gaba ta hanyar girmamawa da moriyar juna.

Akwai buƙatar ƙasashen da suke ganin su shafaffu da mai ne, su dai na ƙoƙarin dawo da hannun agogo baya, domin duniya ta ci gaba. Girmama cikakken ’yancin ƙasa ya zama wajibi a kan kowacce ƙasa babba, ko karama.

Ƙasashen duniya da al’ummominsu sun bambanta, suka san yanayin da suke ciki da manufofi mafi dacewa da su, kuma su kaɗai ne za su san yadda ya kamata su shawo kan matsalolin dake addabarsu.

Don haka, bai kamata a riƙa nunawa ƙasashe fin ƙarfi kan harkokinsu na gida ba, ko kuma a rika nuna musu an fi su sanin abun da ya fi dacewa da su ba.

Kamar yadda Zhang Jun ya bayyana yayin taron, dole ne a samu bambancin ra’ayi daga ƙasa da ƙasa kan batutuwan tsaro, amma ya kamata a samu daidaito ta hanyar tattaunawa da haɗin gwiwa.

Shirin tsaron duniya da shugaban ƙasar Sin ya gabatar ga taron BOAO a watan Afrilu, ya gabatar da wata alkibla ta cimma tsaro na bai ɗaya tare da warware matsaloli masu masu ruwa da tsaki.

An riga an san ƙasar Sin ba mai ƙaunar rikici ba ce, domin an ji, kuma an ga yadda al’ummominta da suka ƙunshi ƙabilu daban daban ke rayuwa cikin jituwa da zaman lafiya, don haka duk wani shiri da za ta gabatar don gane da hakan, a ganina abu ne da ya kamata a karba da hannu bibbiyu, tun da burinta shi ne, gina duniya mai kyakkaywar makoma cike da tsaro da kwanciyar hankali.

Akwai buƙatar sauran ƙasashen duniya su mara mata baya, kuma su ma su yunƙura, su haɗa ƙarfi da ƙarfi wajen ganin an samu ci gaban duniya da kwanciyar hankali, ta hanyar haƙuri da girmama juna da tabbatar da adalci.