Kyan alƙawari cikawa

Daga CMG HAUSA

Akwai wasu mutane 2, ɗaya ya iya magana sosai, amma yakan manta da maganar da ya faɗa, yayin da ɗayan ba ya son magana, sai dai duk wani alƙawari da ya yi, zai yi ƙoƙarin cika shi.

A cikin mutanen nan 2 wanne ka fi so?

Tabbas za a ƙulla abota tare da mutum na biyu ko? Saboda “Alƙawari kaya ne”.

Ba za a iya dogaro kan wani ba, idan ba zai iya cika alƙawari ba.

Wani babban dalilin da ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyar ƙasashen Afirka, shi ne yadda suke iya dogaro da ita, wato yadda take ƙoƙarin cika alƙawarin da ta yi.

Don tabbatar da gaskiyar maganar, za mu iya kwatanta alƙawarin da shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin ya yi, a taron ministocin dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana a birnin Dakar na Senegal, a ƙarshen shekarar 2021, da jawabin da ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya yi, wajen taron jami’ai masu kula da aiwatar da sakamakon taron ministoci na FOCAC, wanda ya gudana a kwanan baya, inda jami’in ya yi bayani kan yadda ƙasar Sin take kokarin cika alkawarinta.

A wajen taron Dakar, shugaba Xi ya ce ƙasar Sin za ta ba kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasashen Afirka lamuni, na cin bashin da ya kai dala biliyan 10 cikin shekaru 3 masu zuwa.

Zuwa yanzu watanni 8 sun wuce, an riga an ba da lamuni na samun bashin da ya kai dala biliyan 3.

Ban da haka, ƙasar Sin ta ba da rance na dala biliyan 2.5, don tallafa wa ƙoƙarin gudanar da wasu manyan ayyuka a ƙasashen Afirka.

A taron da ya gudana a bara, shugaba Xi ya ce ƙasar Sin za ta yi ƙoƙarin shigo da kayayyakin kirar ƙasashen Afirka da darajarsu za ta kai dala biliyan 300 cikin shekaru 3.

Sa’an nan cikin watanni 7 da suka wuce, ƙasar Sin ta riga ta shigo da kayayyaki na dala biliyan 70.6 daga Afirka.

Yayin da a nasu ɓangare, kamfanonin Sin sun zuba jari da ya kai dala biliyan 2.17 ga kasuwannin ƙasashen Afirka, cikin watanni fiye da 8 da suka gabata.

A fannin aikin kiwon lafiya, shugaba Xi ya ce cikin shekaru 3, ƙasar Sin za ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 600 ga ƙasashen Afirka, haka kuma kamfanonin ƙasar da na ƙasashen Afirka, za su yi hadin gwiwa wajen samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 400.

Zuwa yanzu, wasu watanni 8 sun shuɗe, ƙasar Sin ta riga ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 miliyan 189 ga wasu ƙasashe 27 dake nahiyar Afirka, kana kamfanonin ƙasar ta yi kokarin hadin kai tare da takwarorinsu dake ƙasashen Afirka wajen sarrafa alluran, inda ƙarfinsu ya kai samar da alluran rigakafi kimanin miliyan 400 a duk shekara.

Sauran ayyukan tallafi da haɗin gwiwa da ƙasar Sin ta yi alƙawarin aiwatar da su a ƙasashen Afirka, sun haɗa da gina babban ginin hedkwatar cibiyar kandagarkin cututtuka ta nahiyar Afirka, da sauran manyan asibitocin hadin gwiwa, da rage talauci, da raya bangaren makamashi mai tsabta, da aikin tsaro, da dai sauransu, duk ana kokarin ciyar da su gaba, kamar yadda ƙasar Sin ta yi alƙawari a baya.

Me ya sa ƙasar Sin take dora matuƙar muhimmanci kan cika alƙawari?

Saboda babbar manufar ƙasar Sin ta fuskar haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka ita ce, “gaskiya, da daukar takamaiman matakai, da zumunta, da sahihanci”, gami da “dora muimmanci kan adalci maimakon moriya”.

Kana Sin ta tsara wannan manufa ce bisa tushen aƙidarta ta “al’ummar dan Adam mai makomar bai ɗaya”.

A ganin Sinawa, dole ne a yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaban harkoki a ƙasashe daban-daban, kafin a iya tabbatar da makomar bai ɗaya mai haske ta ɗaukacin dan Adam.

Wannan aƙida ta sa ƙasar Sin ke nuna cikakken sahihanci ga ƙasashen Afirka, da ƙoƙarin cika alƙawarinta, yayin da take hulɗa da su.

Fassarawar Bello Wang