Gudunmawar sojojin ga cigaban tsaro da zaman lafiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Bahaushe ya yi wata karin magana da ke cewa, ‘soja birgimar hankaka, kowa ya ga baqin ku zai ga farin ku’. Haka kuma za ka ji yana yi wa soja kirari da cewa, na gwamna ga rawa ga yaƙi! Waɗannan wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen kambama irin jarumta da rawar ganin da sojoji ke takawa, a matsayin su na dakarun tsaron ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.

Matsayin soja a kowacce ƙasa ta duniya ba ƙarami ba ne, saboda kasancewarsa ginshiqin kafuwar kowacce ƙasa. Masana tsarin aikin soja na faɗin cewa, kafuwar tsarin soja shi ne tushen ginin kowacce
al’umma, saboda kasancewarsu garkuwa da ke kare ƙasa daga duk wata barazanar tsaro ko wani hari na makiya da ka iya tasowa, domin yaqi da wanzuwarta da tabbatuwar ’yancinta.

Masanin tattalin arzikin nan Adam Smith a ƙarni na 18 ya rubuta cewa, kafa tsarin soja shi ne aikin farko da ya kamata kowanne jagoranci ya fara mayar da hankali a kai, ba kawai domin maganin maƙiya da abokan adawa na gida da na waje ba, domin kasancewarsu a ƙasa na maganin barazana da karya lagon duk wani yunƙuri na karya doka.

Ƙudiri na 51 na Kundin Haƙƙoƙi na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, haƙƙoƙi ne a kan kowacce ƙasa ta mallaki rundunar sojoji nata na ƙashin kanta, domin tabbatar da ’yancinta da tsaron al’ummarta. Wannan tsaron ’yanci ba ya tsaya kawai ga matakin kare ɗiyaucin ƙasa ba ne, har ma da tsaron dukiya da rayukan ’yan al’umma, tare da tabbatar da kare haƙƙoƙinsu da martabarsu, a matsayinsu na ’yan Adam. Wanzar da zaman lafiya a tsakanin ’yan ƙasa ta hanyar tsayuwar daka wajen hana bata gari da tsagera, amfani da duk wata dama suka samu ta firgita jama’a da haifar da yamutsi a cikin ƙasa.

Wani marubuci John Mroz na da ra’ayin cewa, kasantuwar soja a ƙasa na maganin masu amfani da ’yancin su wajen haifar da barazanar tsaro a ciki da wajen ƙasa. Za a iya ganin haka daga irin yadda dakarun soja ke sadaukar da rayuwarsu a fagagen daga daban-daban, da suka haɗa da yaƙe yaqen Basasa, yaƙi da masu tada ƙayar baya, ’yan ta’adda na cikin gida da na waje, duk domin jaddada ƙarfi da ikon da hukuma ko gwamnatin ƙasa ke da shi.

Masanin falsafa Galtung ya ƙarfafa cewa, ƙaƙƙarfar rundunar soja na tsoratar da duk wasu marasa son zaman lafiya da masu tayar da ƙayar baya, domin samar da cigaba mai ɗorewa a cikin al’umma. Don haka ya ke da muhimmanci kowacce gwamnati ta ba da fifiko wajen ƙarfafa gwiwar jami’anta ta hanyar samar musu da wadatattun kayan aiki, kyakkyawan horo, kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka, da za su ba su damar yin gogayya da ƙwarewa wajen yin arangama da sauran takwarorinsu na duniya.

Ƙarfin ƙasa da tasirinta a duniya na da nasaba da ƙarfin dakarun sojanta, gogewarsu kan dabarun yaqi da ingantattun kayan aikin da ta mallaka. Kamar misalin ƙasar Amurka a duniya ko kuma yadda tasirin Nijeriya ya ke a tsakanin ƙasashen Afrika.

Tarihin harkokin soja da yaƙe-yaƙe a duniya ba zai tava kammala ba sai ya tavo irin gudunmawa da sadaukarwar da sojojin Nijeriya suka riƙa bayarwa tun daga Yaƙin Duniya na ɗaya da na biyu da sauran yaƙe-yaƙe da suka yi ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka da bayan samun ’yancin kan ƙasa a shekarar 1960.

Sannan rawar ganin da dakarun sojan Nijeriya suka taka a ya ke yaƙin basasa na cikin gidan wasu ƙasashen Afrika shi ma babban abin misali ne, duba da yaddasuka yi ruwa da tsaki wajen kawo sauye-sauye a harkokin tsaro, siyasa da zamantakewa na wasu ƙasashen Afrika, irin su Laberiya, Sudan, Mali, Somaliya, da sauran ƙasashe da dama da suka samu kansu a dambarwar siyasa da tawaye da a wasu lokutan suka rikiɗe suka zama yaƙin basasa.

Ko a nan gida Nijeriya ma mun ga yadda dakarun mu suka tunkari matsalar ’yan aware ta Biyafira a wancan karon, waɗanda aka shafe tsawon lokaci tsakanin 1967 zuwa 1970s ana fafatawa da su, wanda a ƙarshe dai aka murƙushe tawayen da suka yi tilas suka miƙa wuya a ƙarƙashin tarayyar Nijeriya.

Ko fafatawa mafi daɗewa ta cikin gida da aka fuskanta ta ’yan ta’addan Boko Haram waɗanda aka shafe tsawon shekaru ana arangama da su tsakanin jihohin Borno, Yobe da Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas, mun ga yadda aka murƙushe tungar su da ke Dajin Sambisa da wasu sansanoni da dama, wanda hakan ya taimaka wajen karya lagonsu da tarwatsa su, abin da ya rusa ƙarfin da a da suke da shi, kuma ya bai wa dakarun Nijeriya damar cimma su da yi musu ɗauki ɗaiɗai.

Haka kuma muna ganin irin dagar da ake ja da ’yan bindiga masu ayyukan ta’addanci da satar mutane ana garkuwa da su da ke fakewa cikin dazukan Jihar Zamfara, Naija, Katsina, Kaduna da Abuja, da kuma wasu ɓangarorin jihohin Nasarawa da Filato.

Waɗannan yaqe-yaƙe da sojojin Nijeriya suka buga da ma wasu da dama da yanzu haka suka zamewa ƙasar nan alaƙaƙai, suna ƙara taimaka musu wajen ƙara gogar da su da ba su damar samun horo da bunƙasa ƙwarewar su ta yaƙi a ɓangarori daban-daban.

Ayyukan da suka gudanar kafaɗa kafaɗa da dakarun wasu ƙasashe, irin su Amurka, Isra’ila, China, Pakistan, Afrika ta Kudu da sauran ƙasashe masu ƙarfin soja yana taimakawa wajen musanyen dabaru da horo, domin sanin yadda ya dace a tunkari kowacce irin matsalar tsaro da ka iya tasowa a ko’ina.

Wani tsohon babban Janar ɗin sojan Nijeriya Chris Garuba ya tava rubutawa a wata lacca da ya gabatar a Kwalejin Yaƙi ta Ƙasa da ke Abuja, cikin shekarar 1997, dangane da ayyukan soja na samar a zaman lafiya bayan yaƙin Basasa, inda ya yi nuni da cewa, fafatawa da ’yan tawaye ko masu tayar da ƙayar baya na kowacce ƙasa na taimakawa dakarun soja samun wasu ƙarin sabbin dabaru da hanyoyin daƙile ta’addanci, sakamakon gogayya da abokan adawa da suke yi da juna, abin da ya kama daga irin makaman da suke amfani da su, aƙidar da suka ginu a kanta, har ma da sanin yadda suke fassara addini.

Tsawon shekaru da sauye-sauyen zamani ya haifar da canji mai yawa a game da yanayin tsarin ayyukan soja a ko’ina a ƙasashen duniya.

Aikin soja ya canza daga rawar daji ko amfani da makami wajen kisa da karya tasirin maƙiya, zuwa masu taimakawa wajen samar da zaman lafiya, cigaban ƙasa da tafyar da shugabanci.

Sojojin Nijeriya sun samu lambar yabo da daman gaske saboda yadda suke ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya a ƙasashe da dama, abin da ya ke gagarar sojojin wasu ƙasashe.

Dubi dai yadda rundunar gamayyar sojojin haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin ƙasar Amurka ta damalmala harkokin tsaro a qasar Iraƙi da Syria, inda aka yi ta fafata yaƙi da asarar rayukan jama’a da dukiyoyi, aka lalata gine-ginen gwamnati da na zaman jama’a, amma samun ingantaccen zaman lafiya ya gagara, saboda abin da aka fi bai wa fifiko shi ne rusa gwamnati da lalata qarfin sojanta.

Haka kuma dakarun ƙasar Saudiyya da haɗin gwiwar wasu ƙasashen Larabawa suka yi ta ɗauki ba daɗi da mayaƙan Houthi na ƙasar Yemen, suna jefa rayuwar ’yan ƙasa cikin ƙunci da tagayyara.

Masana harkokin tsaro na duniya irin su Ken Booth, wanda a shekarar 1991 ya buga wani littafi da a ciki ya yi wani bayani game da sabbin dabarun samar da tsaro, ya yi nuni kan muhimmancin amfani da wasu hanyoyi na siyasa da ƙarfin mulki wajen rage kaifin matsalolin da ke haddasa sojoji ɗaukar makamai da tafiya filin daga don fafatawa da abokan gaba, irin waɗannan dabaru sun haɗa da tsaron dukiya da rayukan al’umma, yin adalci da kiyaye ‘yancin ’yan ƙasa, rage kaifin talauci da samar da ayyukan yi da sauran muhimman buqatun ’yan qasa da za su ɗauke musu hankali daga aikata ɓarna, karya doka ko ɗaukar makami da nufin tayar da ƙayar baya ko tawaye.

Ya ce, samar da tsaro ba ya taƙaita kan amfani da manyan makamai ko amfani da ƙarfin soja ba ne kan masu adawa da zaman lafiya. Tsaro na buƙatar samar wa al’umma cigaba, walwala da ’yanci wajen gudanar da rayuwa… tsaro ba ya samuwa a inda talauci da rashin ayyukan yi, rashin wadatar abinci, rashin ’yanci da nuna wariya suka yi wa jama’a katutu!

Ya zama wajibi gwamnati da jami’an tsaro da ayyukan su ke shafar rayuwar al’umma su haɗa hannu wajen tabbatar da ganin sun rufe duk wata ƙofa da wasu ɓata gari za su yi amfani da ita su haifar da rashin
tsaro da taɓarɓarewar zaman lafiya.

Yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da dabaru na siyasa, diflomasiyya, da shugabanci wajen aiki tare da farar hula, don sauƙaƙa nauyin da ke kan jami’an soja.

Ayyukan da rundunar haɗin gwiwa mai aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato da wasu makwaftan yankuna a jihohin Bauchi da Kaduna ta Operation Safe Haven ke gudanarwa na aiki tare da gwamnati da ƙungiyoyin farar hula yana taimakawa wajen kara wayar da kan jama’a muhimmancin zaman lafiya, rungumar sana’o’i da harkokin wasanni, domin dakushe kaifin ƙiyayya, rashin yarda da juna da ƙyamar sojoji da ya dabaibaye zukatan wasu al’umma a yankin. Hakan kuma ya taimaka ainun wajen samar da ɗorewar zaman lafiya da rage tashin fitintinu.

A yayin da Nijeriya a karo na biyu ke fuskantar wani sabon ƙalubalen tawaye da amfani da makamai kan jami’an tsaro da ofisoshin gwamnati, musamman daga yankin Kudu Maso Gabas, da da sake bayyanar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB ke haifar da sabuwar barazana ga ci gaban haɗin kan ƙasar nan da zaman lafiyar al’ummarta, bayan sauran fitintinu na ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka dabaibaye ƙasar nan, ya zama wajibi ga duk ɗan Nijeriya ya mara wa yunƙurin da rundunar sojojin ƙasar nan ke yi na samar da ingantaccen tsaro da zaman lafiya.

Wannan shi ne zai ba mu ‘yancin cigaba da harkokin mu na rayuwa ba tare da fargaba ba, ya kuma kare mutuncin mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa masu ‘yanci ba ‘yan gudun Hijira ba.

Zan kammala da cewa, aikin soja babbar garkuwa ce da ke kare mutunci da martabar ƙasa, kuma take inganta tsarin zamantakewar al’umma, ba tare da nuna wariya ko ƙyamar wani ɓangare ba.

Da fatan za a yi amfani da sabbin dabarun zamani na tunkarar ‘yan ta’adda da masu tada ƙayar baya, domin kaucewa take haƙƙin waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, da sake raba kan ‘yan Nijeriya.

Allah ya taimaki jami’an tsaron Nijeriya, ya kuma ba mu zaman lafiya mai ɗorewa.