Kannywood: Gyara ta sai ‘yan cikinta – Martani ga Gidan Dabino

Daga KAMAL IYANTAMA

Kamar yadda na yi katari na karanta a wata jaridar Hausa, inda fitaccen marubuci Ahmad Gidan Dabino (MON) ya yi wani ƙayataccen bayani mai cike da alfanu, kuma bayanin ya burge ni.

Kada a ɗauka martanin da na rubuta a sama, martani ne na suka ko kushe, a’a martani na yabawa zan yi wa Gidan Dabino, wato yadda Kannywood ta zama a yanzu abin babu daɗin ji da gani, wanda kuma gyaran ta sai ‘yan cikinta.

Misali; Baturen da zai zo ya ce zai rubuta ma asali da tarihinka a matsayinka na Bahaushe, ai ka san labarin banza ne kuma hauka da naɗe-naɗe za ka gani.

To kamar haka ne a ce wai wasu baƙin haure waɗanda ba ma Hausawa ba ne, magana ma da yaren Hausar sai sun shigo cikin hausawan suke koyo, a ce su ne za su ja ragamar Kannywood? Wannan cikin ba zai haifi ɗa mai ido ba, to haka lamarin yake. 

Idan muka koma baya farkon kafuwar wannan masana’anta, ai Hausawa ne suka kafa ta. Kuma mun ga yadda lamarin ya taho cikin tsari, nasara da ci gaba ta kowane fanni tsawon shekaru.

Kodayake, shigowar baƙi a kowane kasuwanci, harka ko sana’a ba laifi ba ne illa iyaka ma cigaba ne, idan har sun bi tsari, zubi, dokoki da ƙa’idojin wannan kasuwanci.

Malam Ado Gidan Dabino na san ba ka manta ba, a lokacin kuna shugabancin wannan masana’anta kai da abokanka irin su; Malam Ibrahim Mandawari, Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyantama, Ɗan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa da sauransu da yawa, a wancen lokaci lamarin gwanin sha’awa da burgewa, amma banda yanzu.

Wasu baqi waɗanda sai sun shigo cikin Hausawa ma suke iya sanya sutura ta hankali, suke iya harshen Hausa, wai su ne shugabannin Kannywood. An sha kiran taron haɗa kai, amma abin da zai baka mamaki, babu irinku a waɗannan tarukan sai dai ya su, ya su, ke taruwa su sha lemo da naman kaza.

Ina da tabbaci da a ce ku ne ke kan jagorantar Kannywood da tuni mun kere takwararmu ta Kudancin ƙasar nan, tazara mai nisan gaske. Amma yanzu dubi yadda matsaloli kala-kala da ke ta karakaina a cikin harkar, abin ya kai an ma rasa ta inda za a taro su.

Shawarata ba ta wuce a matsayinku na manya har gobe, ku samu lokaci ta amfani da ilimi, hikima da basirarku ku kira waɗancan tsiraru kuma ƙirgaggun baƙin, in ma wasu sun ki zuwa, ku ku je ku same su domin ai durƙusa wa wada ban tunanin zai zama gajiyawa.

Domin manufar abinda ke zuciyarku za ku hanga ba zavinsa ba. A ɗauki kwanaki na musamman domin taunawa da furzawa, tare da bajewa a faifai, rabe aya da tsakuwa, rarrabe tsaki da gari a cikin ilimi.

Kamal Iyantanma Marubu ci ne, kuma manazarci. Ya rubuto daga Jihar Katsina. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *