
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗaruruwan shaguna ne suka ƙone ƙurmus a wata gobara da tsakar dare a ranar Litinin a sananniyar kasuwar Oranyan da ke Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas a Jihar Oyo.
Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar, wadda ta fara ci tun tsakiyar dare, ta shafi shaguna da dama na sassa daban-daban na kasuwar. Sannan, ta shafi ƙananan ‘yan kasuwa da suka haɗa da ‘yan harkar gwala-gwalai, kafintancin zamani, ‘yan gwanjo da wasu kayayyaki.
Shaidu sun ce, wutar da fara ci ne tun da tsakar dare, saidai ba su san ainihin lokacin ba. Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce aƙalla sama da shaguna 200 ne suka ƙone.
An bayyana gobarar a matsayin babban abin tayar da hankali musamman ganin yadda ba a iya gano matakin ɓarnar da ta yi ba.
Mai taimaka wa Gwamna Seyi Makinde na jihar kan gyare-gyaren gobara kuma Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Morof Akinwande, ya tabbatar da faruwar al’amarin a lokacin da wakilinmu ya nemi ji ta bakinsa ta wayar salula. Ya bayyana cewa, ana cigaba da bincike kan musabbabin aukuwar iftila’in da kuma gano matakin damejin da ya yi.
Ya ƙara da cewa, al’amarin ya samo asali ne a lokacin da aka ji wata ƙarar abin fashewa, saidai ba a gano ko gas ne ya yi sanadi ba ko wani abin daban. A cewarsa an yi ƙoƙarin shawo kan al’amarin da misalin ƙarfe 1 na dare domin hana ta cigaba da yaɗuwa.
