Daga USMAN KAROFI
Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa, ya rasa ‘yar sa da kuma ‘ya’yan ta guda uku sakamakon wata gobara da ta cinye dukkan gidan su a safiyar Litinin.
Wanda suka rasu sun haɗa da matar Alhaji Muhammadu Yusuf Bello, sakataren dindindin na ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa ta Jihar Sokoto.
Rahoton da Blueprint ta samu ya nuna cewa wutar ta lalata gidan gaba ɗaya yayin da iyalin suke barci, inda shi kaɗai mijin matar ya tsira.
A lokacin da wakilin Blueprint ya ziyarci wurin, ba a samu tabbacin ainihin sanadin wutar ba, sai dai bincike na ci gaba don gano musabbabin wannan mummunan al’amari.
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Sokoto sun ɗauki awanni da dama suna yaƙi da wutar kafin su samu nasarar kashe ta.
An gudanar da jana’izar waɗanda suka rasu a masallacin Juma’a na garin Sifawa, cikin ƙaramar hukumar Bodinga, inda aka binne su bisa ƙa’idojin addinin Musulunci.
