Bayan shekaru 10, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, a ranar Alhamis, ya musanta dakatar da tsohon gwamnan babban bankin ƙasa, Dr Sanusi Lamido Sanusi, wanda yanzu shi ne Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, bisa zargin cewa dala biliyan $49.8 sun ɓace daga asusun gwamnati.
Jonathan, wanda ya dage kan cewa babu irin waɗannan kuɗaɗe da suka ɓace, ya ce shugabancin CBN a ƙarƙashin Sanusi ya kafa wannan zargi.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis a Abuja yayin ƙaddamar da littafin mai suna “Public Policy and Agents Interests: Perspectives from the Emerging World,” wanda tsohon ministan Kuɗi, Dr. Shamsudeen Usman, wanda ya riƙe muƙamin ministan tsare-tsare a ƙarƙashin gwamnatinsa ya wallafa.
Ya mayar da martani ga gudunmawar da tsohon Gwamnan CBN ya bayar, wanda a cikin littafin ya yi ikirarin cewa an kore shi daga aiki ne saboda ya fallasa ɓacewar kuɗaɗen a ƙarƙashin gwamnatin Jonathan.
Sanusi ya yi tsokaci kan lamarin, wanda ya ci gaba da cewa har ya kai ga korar sa daga muƙamin gwamnan CBN.
A shekarar 2013, Sanusi ya fara magana kan kuɗaɗen shiga na man fetur, wanda ya ce dala biliyan 49 ba a san inda suke ba.
Sai dai daga baya an sake gyara alƙaluman nasa na farko zuwa dala biliyan 20 bayan tattaunawa da ma’aikatar kuɗi.
Gwamnatin Jonathan ta yi gaggawar karyata wannan ikirari, inda wasu sassan gwamnatinsa ke zargin Sanusi da ƙoƙarin yi wa gwamnatin zagon ƙasa.
A watan Fabrairun 2014, watanni kacal bayan ya yi wannan zargin, Shugaba Jonathan ya dakatar da Sanusi. Sai dai kuma da dama daga cikin ‘yan Nijeriya na ganin an dakatar da shi ne da alaƙa da siyasa kuma yana da nasaba da badaƙalar kuɗaɗen da ya fallasa.
Sanusi ya zama Sarkin Kano na 16, an tsige shi a shekarar 2020 kafin a sake maido shi a 2024.
Sai dai a jawabinsa na buɗe taron, Jonathan wanda ya jagoranci ƙaddamar da littafin, ya ce duk da ya amince da ƙasidar littafin kuma ya ba da shawarar a yi bincike, amma bai amince da ikirarin Sanusi na ɓacewar kuɗaɗen ba.
Jonathan ya ce ba a kori Sanusi ba amma an dakatar da shi, ya ƙara da cewa irin waɗannan kuɗaɗen ba za su yi ɓatan dabo ba a Nijeriya, ƙasar da kasafin kuɗinta ya kai kusan dala biliyan 32 a lokacin ba tare da an gano su ba.
Ya kuma bayyana yadda tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tunkare shi a kan lamarin tare da bayyana cewa ba za a iya sace irin waɗannan kuɗaɗen daga wata ƙasa mai fama da matsi na tattalin arziki kuma babu wanda ya sani.
“Sunusi ya bayyana cewa an kore shi ne saboda ya fallasa cewa Gwamnatin Tarayya ta yi asarar dala biliyan $49.8 ba daidai ba ne. Ba a kore shi ba. An dakatar da shi ne saboda kwamitin bayar da rahoto kan harkokin kuɗi ya yi tambaya game da kashe kuɗaɗen da CBN ke kashewa. Kuma akwai manyan laifuka da ya kamata a duba.
Sai dai ya bayyana lokacin da suke bincike wa’adin sa ya ƙare wanda watakila da an kammala da wuri da an dawo dashi
Tsohon Shugaban ya dage cewa babu irin waɗannan kuɗaɗe da suka ɓace. Ya ce ikirarin Sanusi ya fara samun tangarɗa ne lokacin da alƙaluma suka sauya daga dala biliyan 49 zuwa dala biliyan 20 daga baya kuma dala biliyan $12bn.
“
