Gwamnati ta tabbatar da mutuwar mutum 25 a hare-haren Kauru

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 25 sakamakon harre-haren da aka kai a wasu ƙauyuka huɗu a yankin ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Mr Samuel Aruwan, shi ne ya ba da wannan tabbaci cikin takardar ƙarin bayanin da ya fitar ran Laraba a Kaduna.

Kwamishinan ya ce sakamakon harin da aka kai a ƙauyukan Ungwan Magaji, Kishicho, Kigam da kuma Kikoba duk a yankin ƙaramar hukumar Kauru a ranar Talata, gwamnati ta samu ƙarin bayanai kan hasarar rayuka da dukiyoyi da aka samu.

Ya ce da wannan, yanzu adadin waɗanda suka mutu a harin ya ƙaru zuwa mutum 25, mutum uku sun jikkata, an lalata gonaki 68 tare da ƙona bukka 63.

Ya ƙara da cewa, Gwamna jihar, Nasir el-Rufai, ya miƙa saƙon jajantawarsa gami da ta’aziyya ga iyalai da ‘yan’uwan waɗanda ibtila’in ya rutsa da su. Kana ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan sannan Ya maida wa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu dubun abin da suka rasa.

Ya ce gwamnatin jihar ta ba da umarnin Ma’aikatar Bada Agajin Gaggagawa da ta hanzarta haɗa bayanan waɗanda lamarin ya shafa. Tare da cewa, za a rika sanar da jama’a duk halin da ake ciki kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *