A yau Laraba ne ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli Farfesa Joseph Terlumun Utsev ya ƙaddamar da wani kwamitin ƙwararru da zai samar da dabarun daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar nan.
Kwamitin zai yi aikin samar da taswirar inganta madatsun ruwa da tsarin zamantakewa da ma wasu ƙarin shirye-shiryen inganta muhalli cikin gaggawa.
Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu muhimman tsare-tsare guda biyu da suka haɗa da kafa asusun bayar da agajin Ibtila’i da samar da kwamitin yaƙi da ambaliyar ruwa.
Waɗanda suka halarci taron Ƙaddamar da kwamitin sun haɗa da Ministan watsa labarai, Muhammad idris da na Kasafin Kuɗi sanata Abubakar Atiku Bagudu, da ministan Muhalli Balarabe Abbas inda dukansu suka jaddada buƙatar ganin Kwamitin ya fara aiki nan take.
Kazalika gwamatin Shugaba Tinubu ta ware kuɗaɗen tallafin yaƙi da ibtila’in ambaliyar ga ilahirin jihohin ƙasar.
Wannan matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen shawo kan iftila’in ambaliyar ruwa da samar da kariya ta dindindin.
