Fuska mai maiƙo

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Maiƙo a fuska ba ɓoyayen abu ba ne musamman ga mata. A lokacin da ki ka fahimci fuskarki na ƙyali fiye da adadin yanda ki ka shafa ma ta mai, za ki tabbatar da fuskarki na cikin layin fuskokin da ake cewa ‘oily face’ inji bature.

A wannan sati Manhaja za ta kawo wa uwar gida ababen da ke janyo maiƙon fuska da hanyar magance su. Idan kin gyara mu shiga cikin darasin kai tsaye:

Ana samun fata mai maiƙo ta sanadiyyar yawan fitar ‘sebun’wanda ke ƙarƙashin ikon sabashiyos gilans(sebaceous glands) waɗanda ake samu a ƙarƙashin fata. shi wannan sinadari na sibon an halitta shi don ya hana fata bushewar da za ta illata ta. Wannan sinadarin ne idan ya yawaita zai kawo maiƙo da zai iya damun mai shi.

Me ke janyo maiƙon fuska?

Halittar jini ko kuma ince masarrafar ƙwayoyin halitta wato abin da bature ke kira ‘genetic’: Maiƙon fuska abu ne da za a iya gada daga ɗaya daga cikin iyaye. Idan har ya kasance uwa ko uba na tattare da sabashiyos gilan wanda ke aiki fiye da yanda ake buƙata.

Yawaitar shekaru: a lokacin da ki ke ƙara shekaru, kana samun raguwan sinadarin sibon a jiki wanda ke kawo bushewar jiki ga tsofafi.

Ramen gashi mai girma: wani lokaci matsirar gashi da ke jikin fatarmu kan ƙara girma ta sanadiyar shekaru ko ƙara ƙiba da ragewa. Girman ramen gashi na janyo yawaitar sinadarin sibon. Kuma uwar gida ta sani ba za ki iya mayar da ramen gashi ƙarami ba, sai dai za ki iya kula da gefen fatar ki da ke da manyar ramuka ta hanyar busar da su ta amfani da abu mai tsotse matsƙi kamar tawul da tissue.

Amfani da mayukan da fata ba ta so: uwar gida ko kin san rashin sanin irin man da fatar ki ke buƙata na iya janyo yawan matsƙin fuska. Wannan babban magana ce wadda ke buƙatar dogon bayani, saboda uwar gida ta daɗe ta na wankan da bai biya kuɗin sabu ba, ba ko komai ya janyo haka ba face ɗabi’ar da mu keyi ta cuta daban magani daban. Saboda haka ne ma shafin kwalliya zai wa uwar gida alƙawarin warware matsalar ciyar da fatar mu da mu ke yi da abun da ba taso wato shafa mai da ita ba shi ta ke buƙata ba. Don haka ku sa ido ku saurari zuwan darasi kan kayan kula da fata. 

Yawaitar kula da fata: a lokacin da uwar gida ta sha alwashin sai ta raba fatar ta da matsƙi, musamman ma fuska, za ta ɗaura ɗamarar wanke fuska a duk lokacin da ta ga maiƙo ya fito. To uwar gida buɗe kunne ki ji, yawan wanke fuska ba zai magance matsƙi ba, asalima kin kama hanyar ƙaruwan shi, domin shi sinadarin Sabon an haliceshi ne ya fito a lokacin da ya ji fata na bushewa ta hanyar fitar da maiƙo, don haka aikin sa ne ya kula da lokacin da ba ta da matsƙi don kareta daga bushewa, hakan zai sashi aiki fiye da ƙima, wanda kamar yanda mu ka ce ya na ɗaya daga cikin silar ƙaruwar maiƙon fuska. 

rashin amfani da Mai na Hana bushewar fata: a tunanin mu amfani da mayuka masu hana bushewar fata hanya ce ta hana fatar fitar da maiƙo, Sai dai uwar gida ta sani rashin amfani da waɗannan mayuka na ɗaya daga cikin abin da kan harzuƙa sinadarin gurin dagewa da bayyana Kan sa. Mafi a’ala uwar gida ta nemi Man hana bushewar fata marar ƙarfi, wanda tushen sa yafi  ruwa fiye da Mai. wato ‘water based, light wight’ a turance. 

By ukarofi