Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA: Ba ni shawara Asas don Allah. Maigidana na yawan cewa, Ina kama da mamatai. Ba fa fuskata da fuskarta ba, har ga jiki. Yana cewa wai idan na juya Ina tafiya sai in yi kama da ita. Idan yana son ɓata min ma sai ya ce ko fita muka yi sai an ɗauka ni mamatai ce ba mata ba. Idan aka jima bai ba ni haƙƙina ba, sai na yi magana, zai iya cewa, wai wani lokaci yana kunyar kusanta ta saboda kama da surrar jikina ke yi da ta mamatai. Abin ya ishe ni wallahi. Ga shi ni ba wata babba ba da za a ce ta tsufa, haihuwa biyu kawai fa Asas.

AMSA: Cikin baiwa da ni’imar da addinin Musulunci ya yi wa mabiyan shi akwai mafita ga kaso mafi rinjaye na rayuwarsu, tun daga haihuwa, girma, aure, tsufa zuwa mutuwa, babu wanda aka bar mu mu yi a kara zube.

Musulunci ya sanar da mu mafita ga matsalolin rayuwa tun kan su riske mu, don haka mu kan shiga ruɗani ne kawai idan mun ƙi tsayawa mu nemi sanin addinin namu. ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke zama barazana ga rayuwar aure akwai jahilci. 

Iyaye sun fi mayar da hankali wurin kallon irin mijin da suke fatan ‘yarsu ta aura, mai kuɗi ko mai ilimi ko mai kyawawan halayya, amma bai zama babban lamari a wurin su ba sanar da ‘yar tasu abinda ake nufi da aure a Musulunci da kuma hukunce-hukuncen da suka lulluɓe shi. Wannan zai sa duk iliminta na zamani zata zama jahila a gidan miji, saboda tana yin rayuwar ne a yadda ta ga ana yi ko yadda ta mata daidai. Idan ta aikata haramun ma bata sani ba, bare kuma sauke haƙƙoƙin mijin da ke kanta.

Shi kuwa namiji, yayin da ya sallama wa mahaifinsa da zancen aure, tambayarsa kawai “kana da abin auren?” Idan ya tanadi komai, to fa a wurin ka ya isa aure, amma ba ruwan ka da tambayar sa me ya sani dangane da rayuwar aure, ko yadda ake zama da mace da haƙƙoƙin ta. Idan kuwa za ka tambaye shi wataƙila abinda ya sani kawai, ka samu mai dafa ma abinci, wadda za ka mulka a matsayin maigida, ta kawar ma da sha’awa a duk lokacin da ka neme ta, amma fa ita rashin kunya ne ta neme ka a wannan ɓangare. 

Da irin wannan rashin sani ne ake tafka manyan kura-kurai a rayuwa aure, ko ma’aurata su yi abinda ya ɓata auren ma ba tare da sun sani ba, kuma a hakan za su ci gaba da zama tare ba tare da sun san auren na da matsala.

Dalilin da ya sa na kawo wannan dogon zance shi ne, wannan tambaya da ‘yar’wa ta yi, tuni Musulunci ya zayyane mana irin wannan matsala da hukuncin ta, tare da hanyar magance ta, amma rashin sani, ya sa shi da ke aikatawa bai san ma yana aikata laifin da ya haramta masa matarsa har sai ya yi gyara ba. Ita kuma bata san da hukuncin ba, don haka zai iya kusantar ta ba tare da bin yadda addini ya ce ba. Kuma albarkacin ilimin addini zata iya warware wannan matsala da kanta ba sai ta nemi Asas ba, saboda ƙur’ani mai tsarki ya yi bayani kanta ga wanda duk ya nemi sani.

Ba ƙoƙarin mu ganin laifin wani ba, sai dai na yi wannan shimfiɗa ne don ya zaburar da mu kan muhimmancin neman ilimin addini.

‘Yar’uwa wannan lamari naki shi ake kira da ‘zihari’, wato miji ya siffanta matarsa da wani sashe na surrar mahaifiyarshi, ko ya danganta kusantar ta da mahaifiyarshi, kuma hakan ba daidai ba ne a Musulunci, sannan an tanadar ma shi hukunci, wanda zan bayyana da hujja, don kafa misali kan rubutunmu na sama, wato addini bai ɓoye komai ba, kuma ya zama amsar da zata gamsar da mai tambaya da kuma mai karatu ɗari bisa ɗari, saboda kasancewar sa faɗar Allah ba ta Asas ba.

An ruwaito cewa, a zamanin Manzon Allah (S.A.W) wasu maza na yi wa matansu irin wannan ɗabi’a ta siffanta matarsu da mahaifiyarsu, ko ɗaukar alwashin ba za su kusanci matansu ba, suna masu iƙirarin cewa, “idan na kusance ki, tamkar na kusanci mahaifiyata ce,” sukan yi hakan ne don su haramta wa kansu matan.

A cikin haka wata rana, wata mata ta zo wurin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi, tana mai kawo ƙarar mijinta da ke yi mata irin wannan ɗabi’a, take kuma Allah ya ji koken wannan mata, ya sauko da wahayi.

Nana Aisha Allah Ya ƙara yarda da ita, ta ce, “lokacin da matar ta ke bayyana wa Manzon Allah matsalar, Ina daga cikin ɗaki, amma ban ji abinda suke magana kai ba, amma Allah Ya ji har ya amsa mata.”

Shin wacce sura ce wannan?

Za mu ci gaba mako mai zuwa.