Daga ADAMU ADAMU EL-HIKAYA
Dama a na ta batun yin takatsantsan kar yaƙin da Isra’ila ke yi kan Gaza ya faɗaɗa zuwa ƙasashen da ke makwabtaka. Da gaske a ke yi ko dama haka a ke so ya faru gashinan dai yanzu Isra’ila ta aukawa Lebanon da yaƙi. Daga batun yaƙi a kan iyakar Lebanon da Isra’ila ta kudancin Lebanon ko arewacin Isra’ila, yanzu yaƙin ya kai ga har babban birnin Lebanon wato Beirut. Hare-hare da Isra’ila ke kai wa kan Sham na lokaci-lokaci ne kuma ba daga kan wannan yaƙin na Gaza ya fara ba.
Gaskiya ne Hezbollah ta taɓa gwabza yaƙi da Isra’ila amma ba a irin wannan yanayi na dalilin goyon baya ga Falasɗinawa ba. Arangamar baya na da muradi na daban da wannan da ke da zummar murƙushe Hamas da Hezbollah da ma duk ƙasasahen da ke mara mu su baya. In ka ga an ƙyale ƙasa a wannan rigima ba a hararar ta to martanin fatar baki ta ke mayarwa ko kira ta ke yi a yi sulhu. Alamu na nuna inda Afurka ta kudu ƙasar Larabawa ce to tuni an far ma ta da yaƙi kai tsaye ko karaya tattalin arziki don yadda ta ke kushe Isra’ila kan yaƙin Gaza har ma ta kai ƙarar Isra’ila kotun duniya da tuhumar da da kisan ƙare dangi.
Duk da umurnin kotun da ya ba wa Afurka ta kudu nasara bai yi wani tasiri kan Isra’ila ba don yadda ta zama ‘yar mowa a wajen gaggan ƙasashen yamma, duk da haka da za ta iya fuskantar ƙalubalen cewa ta yi karambani. Sarki Abdullah na Jodan da ƙasar sa ke makwabtar ƙud da ƙud da Isra’ila ya shan sharri da hatsarin da ya ke ciki don haka kullum batun sa a yi sulhu don tsayar da yaƙin da kuma nuna sam ba zai bar ƙasar sa ta zama tunga ko fagen yaƙin na Gaza ba. Abdullah na siyasar kadaran-kadahan don da muguwar rawa gwara kin tashi. Idan ya tausayawa Falasɗinawa ainun ba sai an mamaye jodan ba amma shi za a iya mamaye shi ko a gama da shi gaba daya. Babban abun da ya yi namijin ƙoƙari wajen aikatawa shi ne ya shiga cikin jirgi mai saukar ungulu wajen jefa kayan agaji ga al’ummar Gaza.
Katar da ke zama kan gaba tare da Masar wajen jagorantar sulhu tsakanin Isra’ila da Hamas ba ta maida wani martani mai zafi kan kashe marigayi shugaban Hamas Isma’il Haniyeh a Tehran ba. Haniyeh dai na zama ne tsawon lokaci a Doha babban birnin Katar kafin tafiyar ƙaddara zuwa Tehran wajen rantsar da sabon shugaban ƙasar inda a ka kai ma sa hari a ka yi ma sa kisan gilla. Hakan don sanin yanayin siyasar duniya bai sa Katar daina sa baki wajen neman a tsagaita wuta ba. Mu duba Masar da ke da iyaka da Gaza ta Rafah kan yi barara ne kawai cewa ba za ta laumci jibge sojojin Isra’ila kan iyakar ta ba. Yin fito na fito da Isra’ila a zamanin yau na da mummunan sakamako ga kowace ƙasar Larabawa don haka sai dai kin jinin Isra’ila a cikin zuciya. Wasu ƙasashen Larabawan ma sun fi sha’awara haɗa hulɗar diflomasiyya da kasuwanci da Isra’ila maimakon damuwa da lalle sai an kafa ƙasar Falasinawa Larabawa. Siyasa ce ta nuna hakan don neman kauda barar fitina wa imma ga ƙasashen su ko ga ɗorewar mulkin su.
Mu tuna lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ke mulki, ya samu jan ƙasashen Larabawa da dama wajen ƙulla diflomasiyya da Isra’ila a yarjejeniyar da a ka yi wa taken “ABRAHAM” ko “IBRAHIMA” don tuna tarihin asalin Isra’ilawa da kuma Larabawa da Annabi Ibrahim Alaihis Salam. Na tabbata harin da Isra’ila ta kai Sham ya kashe wasu kwamandojin Iran a ginin ofishin jakadanci bai samu fassarar cewa wata takala ba ce ko laifi kuma har yau ba ainhin bayanan ramuwar gaiya kan wannan harin.
Kazalika ko bayan da Iran ta ce ta kai ramuwar gaiya da wasu makamai da ke dauke da wasu makamai da a ka cusa masu tarwatsewa; Isra’ila ta maida martanin hari da ya girgiza sassan Iran da a ke ma ba da labarin Isfahan ne. Nan dai Iran ba ta sake cewa za ta yi ramuwa ba don ta san illar fitowa fili ta shiga yaƙi da wata kasa baranma a ce Isra’ila ce. A yanzu ma ba ta takali Isra’ila kai tsaye ba yaya ta kare. Ga shi cin zalin da Isra’ila ke yi wa Hezbollah ko al’ummar Lebanon amma ba yadda za a yi a ce an taka ma ta birki. Dama Lebanon na cikin mawuyacin halin tattalin arziki sai ga waɗannan hare-hare na Isra’ila. Tamkar targaɗe ne ya koma karaya.
Farkon abun da ɗauki hankali a makon jiya shi ne ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da ke samun goyon baya daga Iran ta lashi takobin ɗaukar fansar wani farmakin na’ura da Isra’ila ta kai inda na’urorin sadarwa mai zango biyu wato oba-oba na ƙungiyar su ka yi ta bindiga a faɗin ƙasar.
Harin ya yi sanadiyyar mutum 9 ciki kuwa har da ‘yar ƙaramar yarinya da ke ’ya ga ɗaya daga shugabannin ƙungiyar.
Kazalika, a wannan farmaki an samu mutum 2,800 da su ka samu raunuka duk da a nan ba bayanai na yanayin tsanantar raunukan. An ga jami’an lafiya na yi wa mutane aikin jinyar raunuka a asibiti kan wasu ’yan ƙananan katifu.
Wani abu da ya tayarwa mutane hankali shi ne yadda a ka ga mutane na yin bindiga a kan tituna don na’urorin da ke jikinsu sun samu hari daga fasahar farmakin.
Wata majiya ta zargi rundunar bayanan sirri ta Isra’ila MOSSAD ta dasa ababe masu fashewa tsawon watanni a na’urori 5000 da Hezbollah ta yi oda daga Taiwan su ka biyo ta ƙasar Hungry.
ƙarin sharhi na nuna zargin yadda Isra’ila ta yi amfani da wasu lambobin kutse ta aikawa na’urorin a lokaci ɗaya inda baturan su su ka yi zafi daga nan su ka tarwatse.
Ban da ma nan cikin Lebanon, na’urorin da Hezbollah ta tura ƙasar Sham masu ɗauke da abun da a ka dasa sun tarwatse.
Hakan ya sanya tsara jawabin gaggawa daga shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah don ɗaukar mataki kan wannan farmaki.
Hezbollah ta ce sam ba za ta daina fafatawa da Isra’ila ba don taimakawa mutan Gaza da sojojin Isra’ila ke gasawa aya a hannu.
Hezbollah ta bayyana kai hare-hare da gomman makamai masu linzami kan filin jirgin saman sojan Ramat Daɓid na Isra’ila.
Hezbollah ta ce wannan martani ne kan miyagun hare-hare da sojan Isra’ila ke kai wa a kudancin Lebanon da ma kulla maƙarƙashiya ga ƙungiyar.
Babban sakataren majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres ya ce ba za su bar Lebanon ta zama fagen yaƙi kamar Gaza ba.
Sakataren ya sha jan hankali kan yadda musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hezbollah ke neman faɗaɗa yaƙin Gaza zuwa wasu ƙasashe ko ma dukkan yankin gabar ta tsakiya.
ƙungiyar Hezbollah ta bayyana shiga sabon babin yaƙi tsakanin ta da sojojin Isra’ila na kan iyaka.
Mataimakin shugaban Hezbollah Na’im Kassem ne ya bayyana haka a jiya Lahadi kan arangamar da ke cigaba tsakanin sassan biyu kan yaƙin Gaza.
Kassem ya ce ayyukan sojojin Isra’ila za su cigaba da jefa rayuwar Isra’ilawa da ke zaune a arewacin Isra’ila cikin yaki har sai an samu tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
Na’im Kassem ya ce kai tsaye za su cigaba da yaƙi da Isra’ila wacce ke ɗaukar Hezbollah a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
Kassem ya halarci jana’izar dakarun Hezbollah biyu Ibrahim Aƙil da Mahmoud Hamad da a ka gudanar a kudancin babban birnin ƙasar Beirut.
Mutanen biyu sun rasa ran su ne a harin da Isra’ila ta kai yayin taron rundunar soja ta musamman ta Hezbollah din mai suna RADWAN.
Zuwa yanzu miyagun hare-haren Isra’ila kan kudancin babban birnin Lebanon, Beirut sun yi sanadiyyar rasa ran mutum 550 ciki da yara 50.
Isra’ila dai ta kara zafafa hare-hare kan sassan da ta ce na ƙungiyar Hezbollah ne da su ke fafatawa da ita kan yaƙin Gaza.
Harin baya-bayan nan ya auna neman kashe shugaban sashen makami mai linzami na Hezbollah ne Abu Jawad Haraka inda harin ya yi sanadiyyar kahe mutum biyu da raunata wasu mutum 11 ciki har da ’yan Iraki.
Rediyon sojan Isra’ila ya ce jirgin yaƙin F-35 ne Isra’ilar ta yi amfani da shi wajen kai hare-haren.
Isra’ila ta ce ba za ta bar Hezbollah ta huta ba don za ta cigaba ne da kai zafafan hare-hare.
Hotunan da a ka yayata sun nuna ɓangarorin jikin mutane a kan motoci gaban ginin da a ka kai farmakin.
Ministan lafiya na Lebanon Firas Abiad ya ce ɗaruruwan hare-haren na Isra’ila sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 558.
Hukumar yara ta Majalisar ɗinkin Duniya, UNICEF, ta ce yara sun ɓace ƙarƙashin gine-gine da su ka ruguje a kan su.
Kammalawa;
Yarima Faisal Al-Turki ya ce Saudiyya ba za ta daidaita dangantaka da Isra’ila ba sai an tabbatar da kafa ƙasar Falasɗinawa.
Al-Turki wanda shi ne tsohon shugaban sashen bayanan sirri na Saudiyya kuma tsohon jakadan Saudiyya a Amurka na magana ne a zauren taron Chattam da ke London.
Yariman ya nuna sharaɗin Isra’ila ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa don hakan ne hanyar kafa hulɗa da Saudiyya.
Ya kamata Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa masu tasiri su ƙara wasu matakai fiye da na fatar baki wajen dakatar da wannan yaƙi daga cigaba da faɗaɗa don kar ƙura ta ɓule sassan yankin da ba a yi tsammani ba.