


Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Rundunar ƴan sanda ta cafke wasu ƴan ƙasashen waje guda uku daga ƙasar Burkina Faso bisa laifin haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya da kuma zargin su da mu’amala da ƴan ta’adda a jihar Zamfara.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Dalijan, ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke baje kolin waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar ranar Laraba.
Ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a dajin ƙaramar hukumar Anka, inda sansanin ɗan ta’addan nan da aka hallaka yake hakar ma’adinai, watau marigayi Halilu Sububu.
Wasu daga cikin abubuwan da aka samu daga hannun waɗanda ake zargin akwai babura goma da manyan kayan aikin haƙar ma’adinai.
Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa, an kuma kama wasu ƴan ta’adda uku da suka fito daga jamhiriyar Nijar ɗauke da bindiga kirar gida mai samfurin AK 47 guda uku.
“Rundunar ta na ƙoƙarin zakulo waɗanda ke kera irin wannan bindigogi na gida ƙirar AK 47 da muka samu a hannun waɗanda mu ke zargin ƴan asalin Kasar Jamhuriyar Nijar ne.”
Haka nan, rundunar ta kama wasu masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba guda goma daga ƙaramar hukumar Talata Mafara tare da buhunan sinadarai da ake sarrafa ma’adinai da dama da suka haɗa da sinadarai na CNI waɗanda suna da haɗari ga rayuwar al’umma a jihar.
Muhammad Dalijan ya ƙara jaddada ƙoƙarinsa na bayar da umarnin tabbatar da cewa haramcin da gwamnatin tarayya ta yi na haƙo ma’adinai yana nan daram a jihar.
“A shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta haramta duk wani aikin haƙar ma’adinai a jihar kuma jami’an mu suna aiki ba dare ba rana domin kama duk wanda aka samu yana karya umarnin da gwamnatin tarayyar ta bayar a kan haka”, inji kwamishinan.
Bugu da ƙari, za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike mai zurfi da rundunar za ta gudanar.
A wata hira da manema labarai jami’in ma’aikatar ma’adinai ta tarayya reshen jihar, Injiniya Samuel Abunuman ya ce, ofishinsa yana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar don tabbatar da duk masu lasisi da masu haƙar ma’adinai da aka dakatar daga dukkan wuraren da ake hakar ma’adanai a jihar basu karya doka ba.
