Sama da mutane 350 suka kamu da cutar Daji a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari Hon.Mustapha Tukur Ruma ya bayyana haka a zauren Majalisar dokoki na Katsina.

Yayi kira ga Majilisar da ta buƙaci gwamnatin jihar da ɗauki matakin gaggawa akan ɓullar cutar a ƙaramar hukumar kada ta bazu a sauran ƙananan hukumomin da suke maƙwabtaka da mazaɓar sa.

Ɗan Majilisar yace,”akwai halin matsi na rayuwa ga kuma wannan annoba,idan kaje asibiti zaka ga masu ɗauke da cutar suke ciki”.

Bayan tattaunawa akan ƙudirin kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya ya buƙaci akawun majalisar daya turawa ɓangaren zartarwa domin ɗaukan mataki cikin gaggawa.

Ɗaukacin yan majalisar sun amince da a hanzarta aikawa gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa domin ceto rayukan al’ummar yankin