Daga USMAN KAROFI a Abuja
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama ta bada belin tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku akan kuɗi naira miliyan 150.
An gurfanar da Ishaku a ranar Litinin tare da Bello Yero, tsohon sakataren dindindin na ofishin kula da ƙananan hukumomi da masarautu.
Mutanen biyu dai na fuskantar tuhuma guda 15 da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Ƙasa ta’annati (EFCC) ta shigar, inda ake tuhumar su da laifin zamba, haɗa baki, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
A yayin da ake gurfanar da su a ranar Litinin, mutanen biyu sun ƙi amsa laifin da ake tuhumarsu da su, sun kuma buƙaci a bayar da belinsu, har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.
Lauyoyinsu, Paul Ogbole, SAN, da Oluwa Kayode, sun gabatar da takardar neman beli.
Babban Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs, SAN, ya nuna adawa da buƙatar belin, inda ya ce dole ne wanda ake ƙara ya shigar da ƙara a hukumance domin ba shi damar amsa yadda ya kamata.
Kotun ta umurci dukkan waɗanda ake tuhuma da su bayar da waɗanda za su tsaya masu mutum biyu, waɗanda dole ne su zauna a babban birnin tarayya.
Mai shari’a Oriji ya hana tsohon gwamnan da wanda ake tuhuma Bello Hero fita ƙasar waje sai da izinin kotu.
Hukumar ta EFCC, ta bakin lauyanta, Rotimi Jacobs, ba ta yi adawa da buƙatar belin tsohon gwamnan ba.
Daga baya mai shari’a Oriji ya sanya ranar huɗu, biyar da 13 ga watan Nuwamba domin fara shari’ar.