Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya Kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi bisa rasuwar mahaifiyar shi Hajiya Maryam Namadi da kuma babban ɗansa Abdulwahab Umar Namadi wanda su ka rigamu gidan gaskiya a ‘yan kwanakin nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwarsu da cewa rashi ne mai kaɗa zuciya ba ga al’umar Jihar Jigawa ba har ma da yankin Arewacin ƙasar nan.
Ya yi addu’ar Allah ya ji ƙansu ya sa jannatul firdausi ce makoma a garesu.
A nasa ɓangaren, Gwamna Umar Namadi ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ta’aziyya da karamcin da ya nuna masa, yana mai fatan kyakkyawan alaƙar su za ta cigaba har ƙarshen rayuwarsu.
