Shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter, wanda ya shahara da ayyukan jin-ƙai ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, a jihar Georgia bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci.

Gabannin mutuwarsa, Charter ya ƙudirin aniyar kaɗa wa ƴar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2024 Kamala Harris ƙuri’a.

Carter ya shugabanci Amurka ne daga shekarar 1977 zuwa 1981 inda ya rasa damar komawa zango na biyu bayan ya sha kaye a hannun Ronald Reagan.

Ya kuma samu kyautar ‘Nobel Prize’ a shekarar 2002.

By Babaji