An tsaurara tsaro akan iyakar Najeriya da Nijar kan ƙishin-ƙishin ɗin harin Lakurawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an tsaro sun tsaurara matakan kariya akan iyakar Najeriya da Nijar kan samun labarin harin mayaƙan Lakurawa musamman a yankin Sakkwato.

Jami’an Hukumar shige da fice (NIS) sun tabbatar wa al’umma cewa kada su ɗaga hankulansu domin sun ɗauki matakan kariya ga shigowa Najeriya ta haramtattun hanyoyi da nufin haddasa fitina.

Wani jami’in hukumar ya tabbatar wa manema labarai cewa NIS da haɗin-gwiwar wasu hukumomi suna aiki tare don shawo kan kowacce matsala da za ta gitta ta kan iyakar.

Haka kuma hedikwatar hukumar dake Abuja, kamar yadda wata majiya ta nuna, ta tabbatar da cewa sabuwar fasar BATTIC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana taimaka wa inganta ayyukan jami’ansu a iyakokin Najeriya ta hanyar bin diddigin ababen da ke faruwa a wurare.

Majiyar ta kuma ce tun lokacin da aka ƙaddamar da BATTIC, ayyukan jami’an da harkokin tsaro ya inganta a faɗin Najeriya.

By Babaji