Gwamna Bala ya ƙalubalanci duk mai binciken ayyukan gwamnatinsa ya je Bauchi 

Spread the love

Daga; BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yayi shaguɓen cewa, ba EFCC ko ICPC ba, koma wace irin hukuma mai bin ba’asin yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a, tazo Bauchi domin yin tozali da ɗimbin ire-iren ayyukan cigaba da gwamnatin sa ta aiwatar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na shekaru shida.

“Ba EFCC ba, kowace irin hukuma ce tazo Bauchi taga yadda gwamnatin mu take gudanar da ayyukan cigaba. An kai koke-koke dabam-dabam daga nan Bauchi zuwa Abuja kan yadda muka gudanar da ginin Gidan Gwamnatin Bauchi”, inji Gwamna.

Sai ya ƙara da cewar, “Kuma ina godewa EFCC da ICPC, suma sun yi mana halacci, sunzo Bauchi sun gani. Sunce wannan aikine ake yi a waɗannan taƙaitattun kuɗaɗe, kuma ake magana akan ƙauran Bauchi, ƙauran Bauchi cigaba da ayyukan ka”.

Gwamna Bala Mohammed yayi wannan jawabi ne a Bauchi a ranar Talata da ta gabata yayin da yake ƙaddamar da ayyukan yin kwaskwarima wa majalisar dokoki ta jihar.

Wannan batu sai da ta kai Gwamnan yin furuci da wasu ayoyin Alkur’ani mai girma, inda yayi karatun abinda mahalicci yake faɗi “Waqal Ja Alhaq, Wa-zahaƙal Baɗilu, Innal Baɗila Kana Zahuƙa” ma’ana idan gaskiya ya fito, ƙarya gushewa take.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewar, gwamnatin sa tana gudanar da ayyukan cigaba ka’in-da-na’in, kuma ba wai bashi da rauni bane a matsayin sa na ɗan-Adam, illa dai yana kawar da kaine wa soki-burutsun jama’a.

Ya kuma ƙara da cewar, “Mutane suna mamakin ina muke samun kuɗaɗen da muke gudanar da waxannan ɗimbin ayyuka na cigaba, muna gudanar da ayyukan ne saboda Allah, kuma bisa tsoron Sa, Kuma bamu tsoron kowane ɗan-Adam, koma wanene, bamu tsoron a kai mu gidan gyara hali, domin mun taɓa zuwa muka fito, kana jama’ar Bauchi suka kawo mu wannan bigere”.

Gwamna ya cigaba da cewar, “Saboda koda za’a yanka wuyan mune, yayi girman da za’a iya yankawa. Duk abinda muke yi, muna yine saboda kyautatawa Jihar Bauchi da al’ummar ta. Domin babu abinda jama’a basu yi mana ba, suda ‘yan majalisu da sauran shugabanni na jam’iyyar PDP, hatta ‘yan jam’iyyar APC sun san gaskiya, har ma godiya suke mana”.

Gwamnan wanda yace a Bauchi kowa ɗan PDP ne, Kuma kowa baƙaurene, ya bayyana cewar, yin kwaskwarima wa majalisar dokokin ta Jihar Bauchi zai laƙume kuɗaɗe jimlar naira biliyan bakwai da ɗigo takwas (N7.8b).

By ukarofi