Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu gungun ma’aikata sun rufe ƙofar shiga ta ma’aikatar kuɗi ta Jihar Zamfara a yau Alhamis a cigaba da zanga zangar lumana bisa abunda suka kira dakatar da albashinsu tsawon watanni shida da gwamnatin jihar tayi.
Da yake zantawa da manema labarai, wani ma’akaci mai suna Aminu Ibrahim ya bayyana cewar su kimanin 776 aka dakatar da albashinsu tsawon watanni shida da suka gabata .
Ya bayyana cewar sunyi duk iya ƙoƙarin su wajen ganin gwamnatin jihar ta saurari kokensu amma abun yaci tura, yana mai nuna alhinin su bisa yadda gwamnatin jihar ta sanya su cikin mawuyacin hali ba tare da samar da mafita a gare su.
“Mun samu mai girma Gwamna Dauda Lawal a watannin baya, ya rantse mana da Allah cewar za a kawo ƙarshen matsalar mu amma har yanzu babu wani mataki daya ɗauka, Kuma har yanzu bamu san matsayin mu ba”.
Ya bayyana cewar, matsalar dakatar da albashinsu tsawon watanni shida, ya tsunduma rayuwar su cikin mawuyacin hali na ƙunci, yunwa da fatara, Yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta dubi halin da suke ciki don ceto rayuwar su.
Idan za’a iya tunawa, a watan Fabrairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar ta bayyana cewar ta bankaɗo ma’auratan bogi su kimanin 2,363, a ƙoƙarin ta na aiwatar da mafi ƙarancin albashin Naira N70, 000.
Ma’akatan sunyi kira ga gwamnatin jihar da ta dubi halin da suke ciki don biyansu albashinsu na tsawon watanni shida da suke bin ta.
