Jami’an NIS sun nemi hana Sanata Natasha fita waje bayan ƙwace mata fasfo a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar ranar Alhamis ne a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja wani al’amari da ke kama da wasan kwaikwayo ya faru a yayin da jami’an Hukumar Shige da Fice (NIS) suka dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga karɓar tikitin jirgin zuwa Landon tare da ƙwace mata fasfo.

Lamarin da ya jefa matafiya a filin cikin al’ajabi da ƙoƙarin samar da tsaiko ga harkokin al’umma.

Wani shaida ya ce, Natasha ta je filin jiragen ne tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan domin fita ta jirgin British Airways.

Saidai, kafin su karɓi tikitin ne kwatsam sai jami’an shige da ficen suka karɓe iko da takardun tafiye-tafiyen nata da faɗa mata cewa tana ɗaya daga cikin waɗanda ke sahun masu barazanar tsaro akansu.

Hakan ya haifar da ruɗani duba da cewa jami’an ba su bada wani gamsassun bayanai game da ƙwace mata fasfo ɗin nata ba.

Akan haka ne cikin nitsuwa Natasha ta fara ƙalubalantar su akan halascin matakin da suka ɗauka akan harkar tafiyar tata.

Ana haka ne sai mijinta nata ya yi ta kiran lambobin wasu wayoyi domin samar da mafita ga halin.

Daga bisani jami’an sun mayar mata da fasfo ɗin nata ba tare da wani bayani ba tare da ƙyale ta ta cigaba da aikin tantancewa, inda daga bisani ta samu kammala hakan cikin ƙanƙanin lokaci.

By Babaji