Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Mazauna garin Maradun a ƙaramar hukumar Maradun kuma mahaifar ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle a Jihar Zamfara na fuskantar babbar barazana ta tsaro daga wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Jummo yayin da ya sanya harajin Naira miliyan 20 ga mazauna garin ko kuma ya kai musu mummunan farmaki.
A cikin saƙon da ya aike wa mazauna yankin na Maradun, Jummo ya buƙaci a bar ’yan bindiga su yi zirga zirga cikin walwala zuwa kasuwanni da dabbobinsu a yankin in har a na so mutane su samu damar shiga gonakinsu.
Ya ƙara da cewa “Babu wani abu da zai hana mu kai hari garin Maradun, bari in faɗa wa mazauna yankin cewa, zan iya neman goyon baya da haɗin kan shugabannin ƴan bindiga 100 da su zo mu haɗu wajen ƙwace garin Maradun a kowane lokaci,” in ji shi.
Ya yi bayanin cewa, domin mazaunan su samu shiga gonakinsu cikin walwala, sai sun tara Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa, kuma idan ba su yi hakan ba, gonakinsu za su ci gaba da kasancewa ba za su iya shiga ba.
Ya ƙara da cewa “Yaranmu zasu riƙa sintiri a yankin sannan su mayar da manoma gida ba tare da yin aiki a gonaki ba”.
Da suke mayar da martani ga barazanar, mazauna yankin sun yi watsi da ra’ayin tara duk wani kuɗi ga ‘yan bindiga .
Wani manomi da ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya kuma roƙi a sakaya sunansa ya ce, babu wanda zai yarda da irin wannan buƙatar na ba ɗan ta’adda Jumbo kuɗi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su ɗauki matakin da ya dace kan maɓoyar ‘yan ta’adda dake a yankin Bayan Ruwa domin bai wa mutane damar shiga gonakinsu.
