Gwamna Buni ya bai wa iyalan Marigayi Sheikh Aisami kyautar gidaje uku

Daga MOHAMMED EL-AMEEN a Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, a ranar Laraba ya raba wa iyalin Marigayi Sheikh Goni Aisami kyautar gidaje.

Mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin addini, Ustaz BG Kyari ne ya gabatar da kyautar a gaban Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulyman.

Manhaja ta jiyo cewa an bai wa matan marigayin kowacce gida, da su ka haɗa da Aisha Badamasi da kuma Hajara Muhammad Ibrahim.

Sannan gwamnan ya bai wa ‘ya’yan marigayin su uku, waɗanda mahaifiyarsu ba ta gidan gida guda ɗaya.

Yayin miƙa takardun gidajen ga iyalan marigayin

Dukkanin gidajen da aka saya suna unguwar Yusufari Bypass, unguwar Isari a garin Gashua, a Ƙaramar Hukumar Bade ta Jihar Yobe, inda kuma an gabatar da takardu.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Bade, Mai Martaba Alhaji Abubakar Umar Sulaiman ya yaba da ƙoƙarin maigirma gwamna a kodayaushe na tallafin gaggawa da kuma tallafa wa al’ummar jihar ta ɓangarori da dama da yake yi.