Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara ta mayar wa alhazai 1,318 Naira 50,000 kowanne

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta mayar wa da kowane mahajjaci daga cikin alhazai 1, 318 da suka yi aikin hajjin bana zuwa ƙasar Saudiyya Naira dubu 50.

Gwamna Bello Matawallle wanda ya bada umarnin mayar da kuɗaɗen, ya umurci hukumar alhazai ta jihar da ta tabbatar da aiwatar da wannan umarni cikin gaggawa.

Ya umurci hukumar da ta fara biyan kuɗin daga nan zuwa ranar Litinin, 12 ga Satumba, 2022 a kowace ƙaramar hukuma 14 na jihar.

Don haka, an shawarci maniyyatan da abin ya shafa da su je ƙaramar hukumar inda suka biya kuɗinsu domin karɓar Naira 50,000 daga ranar Litinin 12 ga Satumba, 2022.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Kabiru Balarabe ta ce matakin na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka na rage wahalhalun tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

Balarabe ya ce gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don tallafa wa jama’a don inganta tattalin arzikinsu, jin daɗinsu da kuma ɗaukaka darajar rayuwarsu da walwala.