Sanata Yahaya ya horas da matasa 60 kan sana’o’in hannu a mazaɓar Kebbi ta Arewa

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirinsa na yaƙi da zaman banza, Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa ya horas da matasa 60 maza da mata sana’o’in hannu da suka haɗa da yadda ake haɗa man shafawa da sabulu da man wankin mota da da robb na maganin amosani.

Da yake jawabi wajen bukin yaye waɗannan matasan a garin Kangiwa a madadin Sanata Dokta Yahaya, Alhaji Sama’ila Dantagago ya ce dalilan da suka sanya Sanata ɗaukar wannan matakin shi ne saboda rage zaman banza da dogara ga gwamnati wanda idan mutum yana da sana’a ba wata barazana da za ta tayar masa da hankali saboda haka yin riko ga sana’a shi ne mafi a’ala musamman a irin wannan lokacin da rayuwa ta yi tsada.

Ya yi kira ga matasan da suka ci moriyar wannan shirin da su yi amfani da ilmin da suka samu wajen kawo cigaban al’umma ta hanyar amfani da kuɗin da aka ba su a matsayin somintavin koyar da waɗansu matasa.

Malama Hasiya tana daga cikin waɗanda suka ci moriyar shirin, ta yaba wa Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi bisa ga ƙoƙarinsa na tuna baya saboda bata tava jin wani ɗan siyasa tana yin haka ba saboda haka ta yi kira ga yan siyasa da su yi koyi da shi.

Abdullahi Muhammad shi ma yana daga cikin waɗanda suka ci moriyar shirin inda ya ba bayyana jin daɗinsa bisa ga irin kulawar da su ke samu daga Sanata Yahaya Mallamawan Kabi.

Ya ce an sha yin irin wannan a baya amma dai sai wannan karon ya samu shiga saboda haka yana godiya tare da alƙawarin amfani da wannan ranar da ya samu.

Aikin koyon sana’o’in da aka gudanar ya ƙunshi qaramar hukumar mulki ta Arewa ne kaɗai kuma an samu wakilci daga kowace mazava yayin da ake jiran sauran shirye-shire da za faɗaɗa zuwa sauran ƙananan hukumomi.