Shirin daƙile ta’addanci don samar da tsaro a makarantu

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka ce gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro da ma’aikatu sun yanke shawarar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance ta’addanci da nufin samar da ingantaccen tsaro a makarantu.

Manufar ita ce a motsa masu ruwa da tsaki don ba da gudummawa ga shirin, don samar da kuɗaɗe da samar da ingantaccen ilimi a Nijeriya. Baya ga samar da tsaro a makarantu ga yara, haka kuma don a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

An fara ƙaddamar da shirin ne mai suna ‘Safe school initiative’ a ranar 7 ga Mayun 2014, don inganta tsaro ɗalibai, malamai da kayan aiki a makarantunmu.

Wannan shiri dai ya biyo bayan sace ɗalibai ’yan matan makarantar Chibok su 276 a Jihar Borno da ’yan ta’addar Boko Haram suka yi a ranar 14 ga Afrilu, 2014. Yayin da aka kuvutar da da yawa daga cikin ’yan matan, amma har yanzu akwai wasu daga cikinsu a hannunsu.

An bayyana shirin ne a taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a Abuja. Gamayyar shugabannin ‘yan kasuwan Nijeriya tare da tsohon Firaministan Birtaniya, Gordon Brown, da wasu sun yi alƙawarin bayar da dala miliyan 10 a lokacin.

Daga baya gwamnatin tarayya ta yi ƙarin alƙawarin dala miliyan 10. Har ila yau, tallafin ya samu daga bankin raya ƙasashen Afirka da ƙasashe irin su Jamus da Norway da Birtaniya. Jihohin Adamawa, Borno da Yobe ne suka fara cin gajiyar shirin.

An yi yunƙurin inganta yankunan da tsaro don samun ilimi, tsara shirye-shiryen gaggawa, da samar da na’urorin sadarwa da sauransu. Amma a halin yanzu, da alama kamar an watsar da shirin.

Abin takaici, abin da muka shaida shi ne yadda ake ta kai hare-hare a makarantu, musamman a Arewa. A watan Fabrairun 2018 ne ’yan ta’adda suka kai hari makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Dapchi a Jihar Yobe inda suka yi awon gaba da ’yan mata 110.

A lokacin da aka sako ’yan matan bayan wasu watanni, huɗu daga cikinsu sun mutu. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su, Leah Sharibu na hannun ’yan ta’adda har zuwa yanzu. A watan Disamban 2020, wasu ’yan ta’addan sun kai hari makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina, sun yi awon gaba da ɗalibai sama da 300 tare da kai su wani daji a Jihar Zamfara.

Daga baya sun sako ɗaliban bayan kwanaki shida a tsare. Daga Kankara ’yan ta’addan sun koma makarantar Kimiyya ta gwamnati da ke Kagara a ƙaramar hukumar Rafi a Jihar Neja inda suka yi awon gaba da ɗalibai kusan 27 da ma’aikatan makarantarsu 15.

Wani ɗalibi ya rasa ransa a cikin hakan. An kuma yi garkuwa da ’yan mata sama da 300 a shekarar da ta gabata a makarantar sakandiren ’yan mata ta gwamnati da ke Jangebe a Jihar Zamfara.

Baya ga makarantun sakandare, ‘yan ta’adda sun kuma yi wa manyan jami’o’i illa. A shekarar da ta gabata, sun kai hari tare da yin garkuwa da ɗaliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Makurdi, Jihar Binuwai, Jami’ar Forestry Mechanization da ke Kaduna da Jami’ar Greenfield da ke Kaduna. Biyar daga cikin ɗaliban jami’ar Greenfield 23 da aka yi garkuwa da su, ‘yan bindigar sun kashe su.

Hare-haren da ake ci gaba da kai wa a makarantu musamman a yankin Arewa ya shafi shiga makarantu, saboda iyaye da dama na fargabar kai ’ya’yansu makaranta.

Hakan dai ya shafi karatu a yankin arewa, domin akwai sama da miliyan 13 na adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, wanda shi ne mafi girma a duniya.

Ya zuwa yanzu dai babu wani ƙoƙari da aka yi na ganin an daƙile wannan mummunar ta’asa da ake yi a makarantun. Duk da cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin daƙile irin waɗannan hare-haren, amma ya kamata su ƙara ƙaimi. Tunda ɗaliban sune makomar ƙasar, akwai buƙatar a tabbatar da tsaro a dukkan makarantun Nijeriya.

Gwamnatin Tarayya na iya ɗaukar sake fasalin tsarin tsaro a matsayin hanya ɗaya ta magance matsalar. Akwai buƙatar mu karkata akalar tsaronmu ko kuma a karkatar da mu domin ana aikata kowane laifi a cikin gida ne. Rundunar ’yan sandan jiha da al’umma za ta inganta tsaron ƙasa baki ɗaya.

Hakanan ya kamata a ƙarfafa sashin leƙen asirin sauran hukumomin tsaro don ba su damar ganowa tare da toshe duk wani laifi da ya faru.

Jama’a kuma za su iya taimakawa wajen isar da bayanan da suka dace ga ‘yan sanda saboda hakan zai ba su damar yin aiki bisa bayanan da suke da su. Ya kamata a kuma yi ƙoƙarin ceto yaran da aka yi garkuwa da su har yanzu.

Jaridar Blueprint Manhaja na yaba wa gwamnoni da hukumomin tsaro bisa sabbin matakan farfaɗo da shirin tsaro a makarantu. Muna ƙarfafa ƙungiyoyi da hukumomi masu ba da gudummawa don su shiga ciki.

Ya kamata a shirya horo kan dabarun tsaro ga malamai da ɗalibai da kuma masu ba da agajin gaggawa. Ilimi ya kasance muhimmin abinda za a sanya a gaba da al’umma za ta amfanaa shekaru masu zuwa.

Duk wani abu da zai tabbatar da ingantaccen ilimi ga ’ya’yanmu a cikin yanayi mai aminci, ya kamata a ƙarfafa shi.