2023: Baya ta haihu a rikicin PDP

*Wike ya cigaba da yi wa Atiku turjiya
…Duk da murabus ɗin Jibril daga shugabancin Kwamitin Amintattun jam’iyya
*Ina nan kan bakana sai Ayu ma ya tafi – Wike
*Jam’iyyar ta naɗa Adolphus Wabara sabon Shugaban Kwamitin Amintattu
*Ruɗani ya taso bayan Gwamna Makinde ya maye gurbin Tambuwal a shugabancin Ƙungiyar Gwamnonin PDP
*Har yanzu Tambuwal ne shugaban ƙungiyar, cewar jam’iyyar
*An naɗa Tambuwal jagorancin yaƙin neman zaɓen Atiku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alhamis da ta gabata Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril ya yi murabus daga muƙaminsa.

Sanata Walid Jibril ya sauka daga kujerar tasa ce a ranar Alhamis, a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin da ta ke ƙoƙarin ɗinkewa.

Ya bayyana cewa, ya yi murabus ne domin kauce wa ƙazancewar matsalar da kuma tabbatar da ganin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya lashe zaɓen 2023.

A halin yanzu dai jam’iyyar PDP da Atiku na tsaka mai wuya, a ƙoƙarinsu na ɗinke varakar da biyo bayan zaɓen Atiku a zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ma ya yi zawarcin kujerar ya bayyana ɓacin ransa kan yadda Atiku ya zaɓi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarsa.

A yayin da Atiku da jam’iyyar ke ƙoƙarshin shawo kansa, Wike dai ya ƙi bayar da kai bori ya hau.

Bai tsaya nan ba, ya yi kira da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Iyiorchia Ayu ya yi murabus daga muƙaminsa, wanda shi kuma ya ce, ba za ta saɓu ba.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ɗin ya ce, murabus ɗin Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP Walid Jibrin ba zai iya dakatar da yunƙurinsa na neman Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam’iyyar ba.

Wike ya bayyana haka ne a wajen taron kwamishina na Ahoada Campus na Jami’ar Kimiyya ta Jihar a ranar Alhamis.

Wike ya ce, jim kaɗan bayan kammala zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a watan Mayu, Alhaji Atiku Abubarkar ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ya ziyarce shi a gidansa da ke Abuja inda ya shaida masa da kansa cewa dole Ayu ya bar muƙaminsa na Shugaban jam’iyyar.

Da muka kammala babban taron mu a ranar Asabar ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zo ya same ni a gidana da ke Abuja ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:30 na safe, Ya ce, min ina so mu yi aiki tare, sai ya ce, ”duba, dole Ayu ya tafi”.

Sai na ce ‘Me ya sa?’ Ya ce, domin idan ɗan takara ya zo daga Arewa, dole shugaban jam’iyya ya fito daga Kudu. Don haka ka aiwatar da abin da ka gaya min. Ina ƙalubalantar zan takarar shugaban ƙasa da ya musanta hakan. Idan ya musanta haka, zan ci gaba da faɗa wa ’yan Nijeriya abubuwa da yawa domin ya isa haka.”

A gefe guda kuma ana zargin Wike da yunƙurin goyon bayan ’yan takarar shugaban ƙasan jam’iyyun APC mai mulki, Bola Tinubu da kuma ɗan takara Jam’iyyar Leba, Peter Obi.

A wani labari kuma, jam’iyyar PDP ta naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, wato Adolphus Wabara, a matsayin Shugabn Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar.

Kodayake naɗin na riƙon ƙwarya ne, hakan ya biyo bayan murabus ɗin da Sanata Walid Jibrin ya yi ne a matsayin shugaban kwamitin.

A ranar Alhamis Jibrin ya ba da sanarwar ajiye muƙaminsa a lokacin da ake tsaka da gudanar da taron kwamitin a Abuja.

Ya ce, ya yanke shawarar ajiye muƙamin nasa ne don warware wasu matsalolin da jam’iyyarsu ta PDP ke fuskanta, musamman kan abin da ya shafi shugabancin jam’iyyar don tunkarar babban zaɓen 2023.

Tun bayan da Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin PDP, jam’iyyar ta soma fuskantar matsin lamba daga ɓangarori mabambanta kan buƙatar Sanata Jibrin da Shugaban PDP na Ƙasa, Iyorcha Ayu su yi murabus daga muƙamansu.

Atiku da Jibrin baki ɗayansu ’yan yankin Arewacin Nijeriya ne.

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zama sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.

Zamowar tasa na zuwa ne biyo bayan ficewar Aminu Tambuwal a taron jam’iyyar PDP na Kwamitin Amintattu da na kwamitin zartarwa na jam’iyyar da ke gudana a Abuja.

Tsohon Shugaban ƙungiyar, Aminu Tambuwal ya sauka ne bayan Shugaban Kwamitin Amintattu, Walid Jibril ya bayyana murabus ɗinsa.

A halin yanzu, tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara ne aka naɗa a  matsayin shugaban riƙo na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP.

Sabbin al’amura dai na zuwa ne da nufin ganin an daidaita yankin kudu, musamman ga mai sun ganin hakan, gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, domin yin watsi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, gabanin zaɓen 2023 mai zuwa.

A wani cigaban kuma, Jam’iyyar PDP ta naɗa Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal a matsayin shugaban yaƙin neman zaɓenta na Shugaban ƙasa.

A baya PDP ta bayyana cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara, ya zama shugaban riƙo na kwamitin amintattu na jam’iyyar, bayan murabus ɗin Walid Jibrin.

An kuma naɗa Wabara a matsayin mai baiwa shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi kira ga shugaban jam’iyyar na ƙasa ya sauka daga muƙaminsa.

Idan za a iya tunawa, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike tare da wasu Gwamnonin Jam’iyyar 4, Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun yi barazanar janye goyon bayan Atiku bayan fitowarsa a matsayin Shugaban Jam’iyyar a 2023. Ɗan takara, matakin da ya savawa tsarin shiyyar da jam’iyyar ta yi.

Baya ta haihu:

Sai dai kuma ana dab da tafiya aikin buga jaridar nan a cikin daren jiya Alhamis, sai Jam’iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP.

Tun bayan murabus ɗin Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, aka yi ta yin cece-kuce.

Sai dai da ya ke mayar da martani kan tambayoyin manema labarai, Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce, ba gaskiya ba ne cewa Tambuwal ya yi murabus.

Aminu Wari Tambuwal

A halin da ake ciki, a wata sanarwar bayan taron kwamitin zartarwar jam’iyyar, jam’iyyar ta ce, “NEC ta amince da tsarin yaqin neman zaɓe na jam’iyyar PDP a faɗin ƙasar a zaɓen 2023, wanda zai fi maida hankali kan cin nasara.”

Sai dai kuma za a bayyana sunayen Waɗanda ke riƙe da muƙaman nan da lokaci kaɗan, inji kakakin jam’iyyar.

Yanzu dai abinda ya rage a gani shine, yadda waɗannan canje-canje da kuma martani da sababbabin matakan da jam’iyyar za ta iya ɗauka gaba ko shi ɗan takararta, Atiku Abubakar, za su iya kawo ƙarshen matsalolinsu na cikin gidan da suka dabaibaye jam’iyyar har su tunkari Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.