Sarauniyar Ingila, Elizabeth, ta rasu bayan shekara 70 a gadon mulki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi daɗewa a kan karagar mulkin Birtaniya, ta rasu a Balmoral tana da shekaru 96. Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 akan gadon mulki Birtaniya.

Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an riƙa nuna damuwa game da yanayin ƙoshin lafiyarta a ranar Alhamis. Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama.

Babban ɗanta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci ƙasar wajen jimami a matsayinsa na sabon sarki da kuma shugaban ƙasashe 14 na ƙungiyar Commonwealth.

A wata sanarwa, Mai Martaba sabon Sarki ya ce: “Mutuwar mahaifiyata abar ƙaunata Mai Martaba Sarauniya, lokaci ne na matuƙar baƙin ciki a gare ni da dukkan iyalaina.

“Muna matuqar jimamin rasuwar Basarakiya abar bege kuma mahaifiyata abar ƙaunata. Na sani cewa rashinta zai matuƙar yi wa ‘yan ƙasar nan da Commonwealth zafi.”

Ya ƙara da cewa a yayin da suke jimamin rasuwarta da kuma sauyin da aka samu, shi da iyalansa za su “nutsuwa da kwanciyar hankali ne bisa sanin cewa duk faɗin duniya ana girmamawa da kuma ƙaunar Sarauniya”.

“Sarki da mai ɗakinsa za su ci gaba da kasancewa a Balmoral da wannan maraice kuma za su koma London gobe,” kamar yadda fadar Buckingham ta shaida.

Dukkan ‘ya’yan Sarauniya sun tafi Balmoral, kusa da Aberdeen, bayan likitoci sun sanya ido sosai kan Sarauniya. Jikanta, Yarima William, shi ma yana can, tare da ɗan uwansa, Yarima Harry.

Firaminista Liz Truss, wacce sarauniyar ta Ingila ta naɗa a ranar Talata, ta ce sarauniyar ”ta samar mana da abubuwan da muke so da kuma ƙarfafa guiwarmu ako da yaushe”.

Ta ce daga yanzu za a san Charles a matsayin Sarki na III.

Mulkin Elizabeth ta II a matsayin sarauniya ya biyo bayan yaƙin basasa, sauyi daga sarauta zuwa Commonwealth, da ƙarshen yaƙin cacar-baka da kuma shiga da kuma ficewar Birtaniya daga Ƙungiyar Tarayyar Turai.

An samu firaministoci 15 lokacin mulkinta fara wa da Winston Churchill wanda aka haifa a shekarar 1874 haɗa da Ms Truss, da aka haifa a 1975, shekara 101 bayan nan.

Ta kasance tana ganawa da firaminista a kowane mako tsawon mulkinta.

A fadar Buckingham da ke birnin Landan, dandazon mutane da ke jiran sanin halin da sarauniyar ke ciki sun barke da kuka bayan jin labarin mutuwarta.

An yi ƙasa-ƙasa da tutar da ke saman fadar da misalin 18:30 na yamma. An haifi sarauniya Elizabeth Alexandra Mary Windsor ne a Mayfair, da ke birnin Landan ranar 21 ga watan Afrilun 1926.

Mutane qalilan ne suka yi tunanin za ta zama sarauniya amma a watan Disambar 1936 kanen mahaifinta, Edward VIII, ya sauka daga sarauta inda ya auri wata Ba’amurkiya, Wallis Simpson, wadda sau biyu aurenta na mutuwa.

Daga nan ne mahaifin Elizabeth, King George VI ya zama sarki, kuma Lilibet, kamar yadda ‘yan uwanta suke kiranta a wancan lokacin da take ‘yar shekara goma, ta zama mai jiran gadon sarautar ƙasar.

By Editor