Mun gano maƙudan kuɗaɗe da kayan sojoji a gidan Tukur Mamu – DSS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa, ta kama kayayyakin da suka haɗa da kakin sojoji da tarin kuɗaɗen ƙasashen waje da dama a gidan Tukur Mamu, ɗan jaridar nan da ke sansanci tsakani da ’yan bindiga.

Kakakin Hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke tsokaci a kan sakamakon binciken da suka yi a gidan mawallafin jaridar nan ta Desert Herald da sanyin safiyar Alhamis.

DSS ta kuma ce, ta kama abubuwa da dama a gidan, kuma da zarar ta kammala bincike za ta maka shi a gaban kotu.

A cewar Afunanya, “yanzu haka, jami’an tsaron sun samu izinin bincike gidansa da ofishinsa, kuma a nan ne aka sami irin waɗannan kayayyakin.

“Sauran kayayyakin sun haɗa da kuɗaɗen ƙasashen waje daban-daban da abubuwan hada-hadar kuɗi.

“Yayin da muke ci gaba da bincike, tabbas za mu gurfanar da shi a gaban kotu,” inji Kakakin na DSS.

Abinda ya faru tun farko:

A safiyar Alhamis, 8 ga Satumba, 2022, jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka mamaye gida da ofishin Tukur Mamu, bayan kama shi a filin jirgin sama na Aminu Kano ranar Laraba.

Mamu, wanda shi ne Mawallafin Jaridar Desert Herald a Kaduna, ya yi sansanci da dama na sako wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a cikin watan Maris ɗin 2022 da aka sace a jirgin ƙasa a Kaduna.

A baya dai Hukumar ’Yan Sanda Ƙasa da Ƙasa (Interpol) ta kama shi a ƙasar Masar a kan hanyarsa ta zuwa ƙaramar hukumar Hajji a ƙasar Saudiyya.

An tilasta masa komawa gida don fuskantar ƙarin tambayoyi daga hukumomin Nijeriya.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, jami’an tsaron ɗauke da makamai sun kai farmaki gidansa da ofishinsa da misalin ƙarfe 12:30 na safiyar ranar Alhamis.

Majiyar ta ce, ’yan sandan sun kama wayoyi da kwamfutocin tafi-da-gidanka da aka gano a harabar.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, an sako matan Mamu da suke tafiya tare da shi zuwa Saudiyya. Sai dai har yanzu ɗansa Ibrahim da sirikinsa Faisal suna hannun jami’an tsaro.

Hukumar gudanarwar jaridar Desert Herald a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta yi Allah wadai da kamen tare da neman a gaggauta sakin mawallafinta ba tare da wani sharaɗi ba.

Makonni da dama da suka gabata, Mamu ya janye daga matsayinsa na jagoran sasantawa wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasan Kaduna. Ya zargi gwamnatin Nijeriya da yi masa barazana.

’Yan ta’addan da suka kai harin jirgin ƙasa na ci gaba da rile wasu fasinjojin.

A halin da ake ciki dai kuma, hukumar ta DSS ta ce an kama Mamu ne bisa zargin sa da hannu wajen karɓar kuɗin fansa da kai wa ’yan ta’addan musanya da waɗanda aka sace.