Nasarawa 2023: Ko rikicin APC zai bai wa jam’iyyun adawa dama?

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Kamar sauran jihohin ƙasar nan da ake sa ran gudanar da zaɓukan gwamnoni na shekarar 2023 dake tafe, a yanzu shirye-shirye da zirga-zirgar siyasa sun yi ƙamari a Jihar Nasarawa inda ‘yan takarar kujerar ta gwamnan jihar a duka jam’iyyu daban-daban ke cigaba da yin duka mai yuwa don tabbatar da sun yi nasarar lashe kujerar wadda a yanzu gwamnan jihar mai ci, Injiniya Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC ne ke zaune a kai. 

Kamar dai yadda aka sani, Gwamna Abdullahi Sule wanda wa’adin mulkinsa zai qare ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023 mai zuwa a yanzu yana kuma neman zarcewa a kujerar karo na 2 a inuwar jam’iyyar ta APC. 

Sauran waɗanda ke son ƙwace wannan kujera mafi girma a jihar daga gun gwamnan sun haɗa da Honorabul David Ombugadu na Jam’iyyar PDP da Abdullahi Maidoya na NNPP da Joseph Ewuga na Labour Party da Umar Akwe Doman a Zineth da Mohammed Inyass na SDP da kuma Mohammed Suleiman na APM. 

Kafin dai a fara kamfen wanda zai bai wa duka ‘yan takarar da magoya bayansu damar zaga lungu-lungu da saƙo-saƙon jihar baki ɗaya don neman goyon baya da ƙuri’un al’ummar jihar, masana harkokin siyasar jihar sun tabbata cewa batuttuwa da za su mamaye kamfen ɗin sun haɗa da batun rashin tsaro da samar da ingantattun muhalli da samar da aikin yi wa ɗimbin matasan jihar da inganta yankunan karkara da dai sauran su. 

Sai dai wani muhimmin abun duba ko yin la’akari anan shine wanna dama na musamman kowanne daga cikin ‘yan takarar ke da shi da zai ba shi damar lashe zaɓen. Wakilin mu a jihar ta Nasarawa, John D. Wada ya gudanar da wannan bincike na musamman don gano tare da bayyana waɗannan dama da kuma da kuma ƙalubale da wasu cikin su ke da shi na lashe zaɓen kamar haka:

Gwamna Abdullahi Sule:

Duk da wasu da dama a jihar na ganin fafatawar zai kasance tsakanin Gwamna Abdullahi Sule da ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa a jihar PDP wato Honorabul David Ombugadu ne kamar yadda aka saba a jihar. Amma wasu masu sharhi akan siyasar jihar da dama na ganin ba shakka bana fa sauran ‘yan takarar daga waɗannan jam’iyyu daban-daban ka iya bada mamaki duk da wasu sun tabbata har ila yau cewa wasu daga cikin su na yi ne don neman suna.

Ba shakka gwamna Abdullahi Sule da jam’iyyar sa ta APC a yayin da za su fara kamfen ɗin su na neman wa’adin mulki karo na 2 za su bai da fifiko ne ga batuttuwa da suka haɗa da tsarin gwamnatinsa a kan tsaron jihar kawo yanzu wanda suka tabbatar yana haifar da ɗa mai ido da kammala muhimman ayyukan cigaba waɗanda gwamnatocin jihar da suka shuɗe suka faro da biya cikakken albashin ma’aikata a kai akai a kuma cikin lokaci. 

Sauran fannoni da gwamnan zai buga ƙirji ya yi alfa’ari da su a yayin kamfen ɗin sun haɗa da kammala gagarumin aikin gina sabon babban filin saukar manyan jiragen sama da samar wa ɗimbin matasan jihar (galibi ‘yan APC) aikin yi ta ƙirƙiro da cibiyoyin koyon sana’o’in hannu a faɗin jihar da dai sauran su. 

Kawo yanzu dai ƙungiyoyin jam’iyyar ta APC a jihar da dama dake yaƙin tabbatar da nasarar gwamnan karo na 2 a nasu ɓangaren suna cigaba da yaɗa cewa lallai gwamnan ya cancanci ƙarin wa’adin idan aka yi la’akari da waɗannan nasarori da gwamnatinsa ta cimma kawo yanzu da a cewar su sun ma wuce samani. 

“Ba shakka shi ne gwamna ɗaya tilo da ke cigaba da tabbatar jihar nan ta samu ɗimbin nasarori a duka matakai kawo yanzu. Kuma mun tabbata cewa idan aka ƙara masa wa’adi 1 kuma ba zai ba mu kunya ba,” cewar ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin ta APC mai suna Asla Martin. 

Sai dai duk da haka akwai shakkun ko jam’iyyar mai ci a jihar za ta iya sake samun nasara a karon nan idan aka yi la’akari da sakamakon zaɓukan fidda gwanayenta da aka gudanar kwanakin baya da ya yi sanadiyyar ficewar wasu jiga-jigan ‘ya’yanta da dama daga jam’iyyar zuwa na adawa daban-daban a jihar. 

Binciken wakilinmu ya gano cewa daga cikin jiga-jigai kuma masu faɗa a ji na jam’iyyar da suka canja sheƙar waɗanda suka qunshi tsofaffin sanatoci da na yanzu dake kujera da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya na da da na yanzu akwai Honorabul Aliyu Wadada da Jonatahn Gaza da Sanata Godiya Akwashiki da Muhammed Agah Muluku da Musa Ibrahim da sauransu da kuma uwa uba wata babbar rigima dake tsakanin Arc. Shehu Tukur da Barista Labaran Magaji akan wanda zai gaji kujerar Sanata daga shiyyar wato na tsohon sanata wanda ya yi murabus wato Sanata Abdullahi Adamu (shugaban Jam’iyyar ta APC na ƙasa a yanzu).

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar na ganin ba shakka hakan zai iya jawo wa gwamnan da jam’iyyar sa babbar cikas a zaɓukan 2023 ɗin.

A yanzu dai lokaci ne kaɗai zai tabbatar ko waɗannan ƙalubale da damar gwamnan za su iya kada shi ko ba shi nasara duk da cewa a yanzu jam’iyyar da shi kansa gwamnan sun yi amannar lashe zaɓen.

Honorabu David Ombugadu na PDP:

Kafin goguwar haɗakar jam’iyyu da suka kafa Jam’iyyar CPC wacce ta ƙwato ragamar mulkin jihar a shekarar 2011, PDP ce ta mamaye jihar ta Nasarawa tun da aka ƙirƙiro da jihar a 1996. Amma tun bayan haɗakar ta CPC, jam’iyyar PDP ta kasance ta adawa wace tana ta iya ƙoƙari da fafatawa ne don tabbatar ta sake ƙwace mulkin jihar gun APC (a yanzu) mai ci. 

Babbar jam’iyyar ta adawa (PDP) ta sake maimaita abinda ta yi a 2011 ne inda ta sake fito da shi Honorabul David Ombugadu wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya ne a matsayin wanda zai sake riƙe tutarta don karawa da gwamnan da sauran ‘yan takarar a 2023 a zaɓen na gwamnan jihar. 

Jam’iyyar ta yi amannar cewa shi (Ombugadu) ne kaɗai zai iya karawa da gwamnan da sauran ‘yan takaran idan aka yi la’akari da ƙwarewarsa a harkokin siyasar jihar da sauransu. 

Har ila yau masu sharhi akan alamuran siyasar jihar suna ganin bana matashin zai iya samun nasara musamman zai iyan amfani da babbar rikicin na cikin gida da APC ke cigaba da fuskanta a yanzu ya kada gwamnan kasancewa a yanzu galibin waɗanda ke ficewa daga APC ɗin suna tare ne zuwa PDP.

Amma fa wani abin la’akari a nan shine yadda ita ma Jam’iyyar PDP a jihar a matsayin ta na babbar jam’iyyar adawa a kuma cikin waɗannan shekaru da dama ta kasa yin amfani da damar ta fito da wanda ya fi ƙwarewa mai kuma farin jini cikin ‘yan takararta da zai iya ƙwato mata muqaminta da APC ta ƙwaton da hakan ba shakka ke dasa shakku a zukatan al’ummar jihar musamman ɗimbin magoya bayanta akan ko za ta iya canja lalen gasar bana?

Joseph Ewuga na jam’iyyar Labour:

Ko da yake binciken wakilinmu ya gano cewa Joseph Ewuga da jam’iyyarsa ta Labour ba a san da su sosai a jihar ba wato ba su yi suna wajen al’ummar jihar idan ana batun siyasa ne.

Amma ga dukkan alamu za su iya bada mamaki idan aka yi la’akari da wani babban gangamin jam’iyyar da suka gudanar a garin Lafiya babbar birnin jihar kwanan nan wanda suka yi mai laƙabin “Takun miliyan 1 na mutum miliyan 1” inda ɗimbin magoya bayansu suka fito ƙwansu da ƙwarƙwata suka bai wa jama’a mamaki ta yawansu da hakan ba shakka ya kasance fargaba ga wasu jam’iyyun a jihar. 

Sai dai wasu na ganin wasan yara da neman suna ne kawai ɗan takaran da jam’iyyar ta Labour a jihar ke yi ba za su kai labari ba.

Alhaji Abdullahi Maidoya na NNPP:

Ko da yake sabon jam’iyyar ta adawa a jihar wato NNPP ta amfana matuqa ita ma da canja sheƙar jiga-jigan APC waɗanda aka ɓata musu rai da dama suka yi kawo yanzu, amma al’ummar jihar da dama na ganin kan takarar nata na kujerar gwamnan jihar wato Alhaji Abdullahi Maidoya ba zai kai labari ba don don bai cancanta ya riƙe tutar jam’iyyar ba. 

Kuma har ila yau binciken wakilinmu ya gano cewa har yanzu jam’iyyar ba ta samun karvuwa da kafuwa a jihar yadda ya kamata ba balle a yi batun ta lashe zaɓen gwamnan jihar. 

Sai dai ba zai zama abin mamaki ba idan ta lashe zaɓukan wasu muƙaman siyasa a jihar a lokacin zaɓukan gama-gari na 2023. 

Shi dai Alhaji Abdullahi Maidoya fitaccen ɗan kasuwa ne da ya yi suna sosai amma a garinsa na Lafiya babban birnin jihar ce aka fi san shi. Amma duk da hakan damar samun nasarar sa bai da yawa.

Mohammed Inyass na SDP:

Mohammed Inyass shi ne ɗan takarar kujerar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar SDP wacce ake wa laƙabi da mai alamar doki. Ita ma jam’iyyarsa binciken wakilinmu ya gano cewa ta amfana da canje-canjen sheƙar masu faɗa a ji na APC ɗin a jihar daidai gwargwado da hakan ke ƙara bunƙasata da kuma damarta na lashe zaɓen. Ba shakka shi ma zai iya bada mamaki a baɗi. 

Sai dai babban ƙalubalen jam’iyyar da shi kansa Mohammed Inyass shine kasancewar ta sabuwar jam’iyya a jihar wacce al’ummar jihar da dama ba su ma san da ita ba kafin zuwan Honorabu Aliyu Wadada cikinta wanda ya kasance jigo a APC kafin ya canja sheƙarar. 

A taƙaice dai waɗannan sune ƙalubale da damar da kowanne daga cikin ‘yan takaran jam’iyyun daban-daban a jihar waɗanda suka gabatar da waɗanda za su riƙe musu tuta a zaɓen gwamnan jihar na 2023 dake tafe ke da shi a jihar dangane da zaɓen.