Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A yayin da damina ke kwararowa gwamnatin Katsina ta fara raba takin zamani ton 20,000 ga manoma a jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya ƙaddamar da rabon takin a ƙaramar hukumar kusada a inda ya bayyana cewa ya cika alƙawarin da yayi na rabawa manoma takin zamani kafin faɗuwar ruwan sama a wannan damina na bana.
Ya bayyana a wajen bikin cewa irin wannan tallafi da gwamnati ta samar a bara ya bunƙasa amfanin gona ga manoma.
Raɗɗa sai yayi kira ga manoma a jihar da su rinƙa amfani da dabarun noma na zamani domin bunƙasa noma.
Ya sanar da cewa za su kai wannan taki a kowace rumfar da ke jihar “kuma za’a sayar da takin a farashi mai sauki na rabin kuɗin da ake sayar da shi a kasuwa”Dikko ya ce.
Gwamnan ya ce bayan takin zamanin da gwamnati za ta raba wanda ya kai buhu 40.000 , akwai cibiyar samar da kayan aikin gona da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙaddamar mai ɗauke da taraktoci 400 da sauran kayan aikin na zamani.
Ya bayyana cewa wannan taraktoci za’a riƙa bada su haya ne a manoma,kuma kowane manomi zai amshi haya ,idan ya kammala aikin noma ya dawo da ita.
Malam Dikko yace gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin kauce ma abin da ya faru a baya da wasu manya suka handame,wasu kuma suka sayar a wasu jiha.
Ya ce kowace ƙaramar hukuma a jihar za ta amfana da shirin.
